Yan Bindiga Sun Sace Malamin Jami’ar tarayya a Zamfara
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani malamin jami'ar tarayya da ke Gusau, jihar Zamfara
- Wani da abin ya faru kan idonsa, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun sace malamin ne a cikin gidansa a safiyar ranar Laraba
- An ruwaito cewa 'yan san sun kawo daukin gaggawa don hana 'yan bindigar tafiya da malamin amma hakan ba ta yiyu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani daraktan cibiyar bincike na jami’ar tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, mai suna Bello Janbako.
Janbako, babban malami ne a sashen nazarin addinin Musulunci na jami’ar, wanda aka yi garkuwa da shi a gidansa da ke Damba a Gusau, babban birnin jihar a ranar Laraba.
Wani mazaunin yankin mai suna Nasamu Garba ya shaidawa The PUNCH cewa ‘yan bindigar sun shiga gidan Janbako ne da misalin karfe 2 na safiyar Laraba inda suka tafi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan bindiga suka sace Malam Bello Janbako - Garba
Garba ya ce jami’an tsaro sun yi artabu da ‘yan bindigar a wani yunkuri da suka yi na dakile sace malamin.
Ya ce:
“Lokacin da ‘yan bindigan suka isa gidan Bello Janbako, sun yi harbe-harbe domin tsoratar da mazauna yankin.
“Daga baya sun kutsa cikin gidan malamin suka yi awon gaba da shi amma suka yi kicibis da jami’an tsaro a hanyarsu ta fita anguwar, inda suka yi musayar wuta."
Garba ya kara da cewa duk da kokarin jami’an tsaro, ‘yan bindigar sun yi galaba a kansu saboda yawan su inda suka gudu zuwa daji tare da Bello Janbako, rahoton News Now.
Masu garkuwa sun addabi yankin da sace-sace
Ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar tsaro a yankin, inda ya ce duk da kusancin su da gidan gwamnati na Gusau hakan bai hana yawan kai hare-hare da sace-sace a yankin ba.
Rahotannin sun bayyana cewa ko a kwanaki biyu da suka gabata, sai da aka yi garkuwa da wani daraktan kudi a ma’aikatar kudi ta jihar wanda ke zama a yankin.
Bugu da kari, a shekarar da ta gabata ma an sace mata da ’ya’yan wani daraktan kudi, Surajo Hassan.
NSCDC ta kama matashin da ya kona gidaje a Gombe
Hukumar tsaron ta NSCDC ta ce ta samu nasarar cafke wani matashi da ake zargin ya bankawa gidaje hudu wuta a kauyen Dele Jesus da ke jihar Gombe.
Rahotanni sun bayyana cewa matashin mai shekaru 27 ya kona gidajen ne bayan wata hatsaniya da ya samu da dan uwansa, lamarin da ya kai ga yin barnar.
Asali: Legit.ng