Aikin Dan Sanda: Dan Majalisa Ya Bankado Yadda Ake Korar Hausawa Yayin Tantancewa a Jos
- Yayin da ake ci gaba da tantance matasa masu sha'awar shiga aikin dan sanda, an fara samun matsaloli a jihar Plateau
- Wani dan majalisar jihar, Hon. Adamu Aliyu ya yi zargin cewa ana korar Hausa/Fulani daga wurin tantancewar da cewa ba 'yan Jos ta Arewa ba ne
- Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Alfred Alabo bai yi martani game da zargin dan Majalisar ba har zuwa wannan lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Dan Majalisar jihar Plateau ya bankado wata badakala da ake korar Hausa/Fulani a yayin tantance masu neman aikin dan sanda.
Hon. Adamu Usman ya yi korafin ne yayin da ake korarsu a karamar hukumar Jos ta Arewa cewa ba 'yan yankin ba ne.
Mene ake zargin 'yan sandan da aikatawa?
Wannan ya biyo bayan ci gaba da tantance masu neman shiga aiki dan sanda a babban ofishin hukumar da ke birnin Jos a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Aliyu ya yi wannan korafin ne a ofishin kakakin rundunar a jihar bayan samun korafe-korafe daga 'yan yankinsa.
Ya ce matasan sun fada masa cewa wasu daga cikin masu tantancewar su na korarsu da cewa su ba 'yan yankin ba ne, cewar Blueprint.
Dan majalisar ya tabbatar da cewa hakan ya sabawa 'yancin matasan da suke da shi kuma hakan nuna wariya ne.
Ya ce zai bi duk hanyar da ya dace don ganin wadannan matasa sun samu aikin kuma sun taimaka wa kasa wurin dakile matsalar tsaro.
Wane martani rundunar ta yi?
A cewarsa:
"Ina kira da ga hukumar 'yan sanda da ta yi duk abin da ya dace don ganin ba a cire sunayen mutanenmu ba.
"Ina kuma kira ga hukumar ma'aikatar 'yan sanda ta shiga lamarin, bai kamata tun yanzu a fara nuna wariya a daukar aiki na Gwamnatin Tarayya ba."
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Alfred Alabo bai amsa kirar waya da Daily Trust ta aike masa ba.
Alummar Musulmi sun yi addu'a ga Gwamna Caleb
A wani labarin, al'ummar Musulmai a Jos sun yi addu'ar samun nasara ga Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau.
Mutanen sun ja ayoyin Alkur'ani tare da yi wa gwamnan addu'a da cewa ba ya nuna musu wani wariya a cikin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng