Hankula Sun Tashi Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Mutum 85 a Hanyar Kaduna-Abuja
- Masu garkuwa da mutane da ake zaton yan bindiga ne sun dawo da ayyukansu a kan titin Kaduna zuwa Abuja
- Duk da tsauraran matakan tsaro da ke wajen, mazauna sun bayyana cewa yan ta'addan sun toshe hanyar sannan suka sace mutum 85 a Kaduna cikin kwana 4
- A halin da ake ciki, rundunar yan sanda ta karyata rahotannin cewa yan bindigar sun sace mutane da dama hanyar Kaduna zuwa Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kaduna, jihar Kaduna - Rahotanni sun kawo cewa an yi garkuwa da a kalla mutane 85 yayin da yan bindiga suka kai hare-hare garuruwa da dama a jihar Kaduna.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, hare-haren sun gudana ne tsakanin Alhamis, 4 ga watan Janairu da Lahadi, 7 ga watan Janairu.
Yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna Kaduna da dama
Jaridar ta bayyana cewa wakilanta da suka ziyarci titin Kaduna zuwa buja a Dogon Fili kusa da Katari a jihar Kaduna, a ranar Talata, 9 ga watan Janairu, sun tattaro cewa kimanin matafiya sama da 30 aka sace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma tattaro cewa wasu rukunin yan bindiga sun kuma yi awon gaba da wasu mutum 55 a garuruwa uku da suka hada da Dudumishini, Badoko, da Kwakware duk a yankin Katari.
Yohana Sarki Hakimin Bishini wanda ya kunshi Katari, Doka, Ariko, Kworotsho da sauran kauyuka ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sarki ya ce:
"Kafin harin na ranar Lahadi, yan bindigar da yawa sun farmaki wasu kauyukan da ke kusa da yankin Katari tare da yin garkuwa da mutane da dama."
Rundunar yan sanda ta yi martani
A halin da ake ciki, rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da cewar yan bindiga sun kai hari titin Kaduna zuwa Abuja a Dogon Fili kusa da Katari.
Sai dai kuma, rundunar ta yi tsit kan sace matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Jaridar Premium Times ta nakalto Mansir Hassan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna yana cewa:
“An yi artabu sosai a hanyar Kaduna zuwa Abuja tsakanin jami’an tsaro da yan bindiga a ranar 6 ga watan Janairu da karfe 23:30 ko kusa da haka.
"Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan bindiga da dama suka yi yunkurin tsallaka titin Dogon Fili inda suka doshi hanyar Jere, sannan jami’an tsaro suka bude wutatare da tarwatsa yan bindigar.”
Sojoji sun ragargaji yan bindiga a Kaduna
A wani labarin, mun ji cewa tawagar farko ta rundunar sojin kasan Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kwato makamai da babura a hannun 'yan ta'adda a jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Musa Yahaya, mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar, ya tabbatar da nasarar farmakin.
Asali: Legit.ng