Shugaba Tinubu Ya Nada Majalisar Gudanarwa Ta NAHCON, Fitaccen Malamin Kano Ya Shiga Ciki
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabuwar majalisar gudanarwa ta hukumar NAHCON zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta tabbatar da su
- Shugaban hukumar, Jalal Arabi, yana nan a kan kujerarsa a matsayin shugaban hukumar inda Aliu Abdulrazaq zai yi aiki a matsayin Kwamishinan manufofi, ma'aikata da kudi
- Shugaba Tinubu ya ce ya amince da nadin ne domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2024 ba tare da matsala ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabuwar majalisar gudanarwa ta hukumar jin dadin Alhazai ta kasa (NAHCON).
Majalisar dattawan Najeriya ce za ta tabbatar da sabbin nade-naden.
Tinubu ya nada mambobin majalisar gudanarwa ta NAHCON
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ajuri Ngelale, kakakin shugaban kasa ya saki a yammacin ranar Laraba, 10 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Tinubu ya nada mutanen ne a cikin "kudurinsa na tabbatar da aikin Hajjin 2024 ya tafi daidai ba tare da matsala ba."
Ga jerin mutanen da aka nada a hukumar aikinb hajjin:
Jalal Arabi — Shugaba (a ofis)
- Prince Anofi Elegushi — Kwamishinan ayyuka
- Aliu Abdulrazaq — Kwamishinan manufofi, ma'aikata da kudi
- Farfesa Abubakar Yagawal — Kwamishinan tsare-tsare da bincike
Wakilan yankin
- Muhammad Umaru Ndagi — Arewa ta tsakiya
- Abba Jato Kala — Arewa maso Gabas
- Zainab Musa — Kudu maso Kudu
- Farfesa Musa Inuwa Fodio — Jama’atul Nasril Islam
- Sheikh Muhammad Bin Othman — Arewa maso Yamma
- Tajudeen Oladejo Abefe — Kudu maso Yamma
- Aishat Obi Ahmed — Kudu maso Gabas
- Farfesa Adedimeji Mahfouz Adebola — Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya
Gwamnatin Tinubu ta sanar da kudin Hajji
A gefe guda, mun ji a baya cewa gwamnatin tarayyan Najeriya ta sanar da cewa maniyyata za su biya Naira 4.5m kan kowace kujerar hajji ɗaya domin aikin Hajji mai zuwa na shekarar 2024.
Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa (NAHCON) ce ta bayyana sabon farashin kujerar aikin hajjin ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023.
NAHCON ta wallafa sanarwa a shafinta na Facebook cewa Musulmai masu niyyar sauke farali a 2024, za su biya Naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin hajji.
Asali: Legit.ng