Ministan Abuja Wike Ya Yi Kicibis da Abokin Karatunsa Na Sakandare, Ya Yi Masa Kyautar Kudi a Bidiyo

Ministan Abuja Wike Ya Yi Kicibis da Abokin Karatunsa Na Sakandare, Ya Yi Masa Kyautar Kudi a Bidiyo

  • Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike ya ba wani abokin karatunsa na sakandare kyautar kudi
  • Wike ya yi kicibis da abokin karatun nasa ne a yayin da ya ziyarci mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Victor Giadom, a karamar hukumar Gokana da ke jihar Ribas
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ziyarci Giadom domin dinke baraka tare da daidaitawa da jigon jam’iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya hadu da wani abokin karatunsa na sakandare a yayin ziyarar da ya kai wa mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Victor Giadom, a karamar hukumar Gokana da ke jihar Ribas.

A lokacin da yake jawabi ga jama’a a yayin wani taron siyasa, tsohon gwamnan na jihar Ribas ya hango abokin karatunsa na sakandare kuma nan take ya isa gare shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kori dukkan kwamishinoni da hadiman gwamnatinsa a arewa, ya faɗi dalili

Wike ya yi wa abokin karatunsa kyautar kudi
Ministan Abuja Wike Ya Yi Kicibis da Abokin Karatunsa Na Sakandare, Ya Yi Masa Kyautar Kudi a Bidiyo Hoto: Nyesom Wike - CON
Asali: Facebook

A bidiyon wanda @tvcnewsng ya wallafa a dandalin X (wanda aka fi sani da twitter a baya), ministan ya ba abokin karatun nasa kyautar kudi sannan ya fada ma magoya bayansa cewa makarantar sakandare daya suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya sun yi martani

@poshtimms

"Shin wannan zai fitar da shi daga talauci? Mulki, kudi, matsayin da sanayya yana da tasiri sosai, kuma yana rarraba mutane zuwa nau'i daban-daban.

@Asiwajuson23

"Kawai ka gina alakar da ta dace da kowa a rayuwa. Baka san ya gobe za ta kasance ba. Labarinsa na shirin canjawa

@Omeke_Nelson_C

"Shin dole ne sai mutumin ya durkusa a kasa?..Ya kamata Wike ya gayyace shi ofishinsa don karin ci gaba."

Omokri ya kwatanta mulkin Tinubu da Buhari

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya yaba ma Shugaban kasa Bola Tinubu kan manyan matakan da ya dauka kan al’amuran kasar cikin mako guda.

Kara karanta wannan

Yana dab da sauka mulki, Gwamna Bello ya naɗa sabbin shugabannin ƙananan hukumomi kan abu 1

Omokri ya yaba ma Tinubu kan dakatar da ministar jin kai da yakar talauci, Betta Edu kan badakalar kudi naira miliyan 585 a ma’aikatarta.

Ya kuma bayyana cewa, wadannan nasarori guda 11 da Tinubu ya samu cikin mako guda da ace magabacinsa ne, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, da sai ya shafe tsawon shekara guda kafin ya cimma masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng