Bayan Shekaru 13, Tinubu Ya Amince a Biya Iyalan Sojojin da Su ka Mutu N18bn

Bayan Shekaru 13, Tinubu Ya Amince a Biya Iyalan Sojojin da Su ka Mutu N18bn

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sake yin magana game da hakkokin sojojin da su ka mutu a Najeriya
  • Janar Taoreed Lagbaja ya ce shugaban kasa ya yarda a biya kudin inshoran sojoji na fiye da Naira biliyan 18
  • Shugaban hafsun sojoji ya sanar da haka da ya ziyari dakarun ‘yan sandan Najeriya a jihar Enugu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban hafsun sojojin kasa ya ce Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin da zai sharewa dubban mutane hawaye.

Laftanan Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana cewa shugaban kasa ya amince a biya hakkokkin iyalan sojojin da su ka mutu.

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai biya hakkokin sojoji Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya share hawayen iyalan sojoji

Janar Taoreed Lagbaja ya ce an dauki tsawon lokaci ana jiran wadannan makudan kudi, Sahara Reporters ta fitar da rahoton.

Kara karanta wannan

Badakalar Kwangila: Mutane sun dage dole a fatattaki Minista na 2 a Gwamnatin APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimakawa shugaban kasa a kafofin zamani, Olusegun Dad ya ce Bola Tinubu ya amince a biya iyalan sojojin N18.4bn.

Kamar yadda hadimin na Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya shaida a dandalin X, tun shekarar 2011 ake jiran a biya kudin.

Gwamnatin Tinubu za ta kashe N30bn

Abin ban sha’awar shi ne kwanan nan shugaba Bola Tinubu ya yarda a saki bashin alawus da albashin ‘yan wasan Super Eagles.

Kungiyar ‘yan kwallon Najeriyan su na bin gwamnatin tarayya bashin Naira biliyan 12.

Segun Dada ya ce matakin da shugaban kasa ya dauka zai kara karfin gwiwar jami’an tsaron da ke kokarin kare Najeriya.

Ana yabawa Shugaba Tinubu a X

Da wannan umarni da Bola Tinunu ya bada, jama’a su na ta tofa masa albarka a X.

Wale Adedayo ya ce:

Kara karanta wannan

"Burin kowane ɗan Najeriya ya ɗauki hoto da ni" Ministan Tinubu ya yi magana mai jan hankali

"Madalla, shugaban kasa."

Wani mai aski a garin Osogbo kuwa cewa ya yi:

Kai, wannan abin ya yi!”

Injiniya Abdul Basit Afolabi ya jinjinawa shugaba Bola Tinubu.

A cewar Adebayo da @Thatuniquebro:

“’Yan adawa za suyi kamar ba su ga labarin ba.”

Omo Osun ya ce mijin kanwarsa ya mutu a 2014 ya bar mata yara biyu, yanzu matar ta rasu ba tare da an biya ta hakkokin ba.

Addu’arsa shi ne kakannin yaran su karbi kudin a madadin yaran, mahaifinsu ya mutu ne wajen yaki da Boko Haram a Borno.

Atiku ya yabi shugaban kasa Tinubu

Atiku Abubakar ya yabi gwamnatin APC da aka yi waje da Betta Edu domin ayi bincike a kan ta, dazu aka kawo maku rahoton.

Wazirin Adamawa ya ce kudin talaka sun zama ATM da POS na yin sata a gwamnatocin Muhammadu Buhari da Bola Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng