PDP Ta Taso Tinubu a Gaba Ya Dakatar da Minista Na 2 a Gwamnatinsa, Ta Fadi Dalili

PDP Ta Taso Tinubu a Gaba Ya Dakatar da Minista Na 2 a Gwamnatinsa, Ta Fadi Dalili

  • Jam’iyyar PDP ta buƙaci a gaggauta dakatarwa tare da binciken ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo
  • Hakan na zuwa ne kan zargin Tunji-Ojo na da hannu wajen samun kwangilar N438m a wajen Betta Edu
  • PDP ta ce abin da ministocin biyu suka yi ba abin da za a yi uzuri a kansa ba ne kuma dole su fuskanci hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP a ranar Talata, 9 ga watan Janairu, ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya gaggauta “sauke” ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo daga muƙaminsa.

Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta, Debo Ologunagba, ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike tare da gurfanar da Tunji-Ojo a gaban kuliya.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Minista ya magantu bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa, bayanai sun fito

PDP ta bukaci Tinubu ya sauke Tunji-Ojo
PDP na son Tinubu ya dakatar da Tunji-Ojo Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo
Asali: Facebook

Sunan Tunji-Ojo ya fito a badaƙalar Betta Edu

A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan zargin karkatar da N585m da dakatacciyar minista Betta Edu ta yi, an taso Tunji-Ojo a gaba kan zargin karya dokokin aikin gwamnati da suka shafi kwangila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi Tunji-Ojo da yin amfani da ofishinsa wajen samar da kwangila ga kamfanin New Planet Project Limited, wanda ya kafa.

Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin New Planet Project Limited na ɗaya daga cikin kamfanonin da suka samu kwangilar sama da N2bn daga wajen Betta Edu.

Wata takarda da ke yawo (wacce ba a sanya hannu ba) ta nuna cewa an biya kamfanin New Planet Project Limited N438m a matsayin kuɗin kwangilar.

Hakan dai ya janyo cece-kuce daga ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta, musamman a X (tsohon Twitter), inda wasu suka yi kira da a hukunta shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kira wani minista zuwa Aso Villa kan badaƙalar N438m da Betta Edu, bayanai sun fito

Wacce buƙata PDP ta nema?

Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya PDP ta shiga sahun masu yin wannan kiran.

Wani ɓangare na sanarwar PDP na cewa:

"Ci gaba da zaman Olubunmi Tunji-Ojo a matsayin ministan harkokin cikin gida zai ƙara tabbatar da matsayin PDP na cewa gwamnatin APC da Tinubu ke jagoranta ta zama mafakar masu wawure dukiyar ƙasa.
"Hanya ɗaya tilo da Shugaba Tinubu zai ba ƴan Najeriya tabbaci ita ce ya gaggauta sauke ministan harkokin cikin gida tare da bayar da damar gudanar da bincike kan yadda aka fitar da N438m.
"Hakan zai sanya a bankaɗo duk wasu masu hannu a badaƙalar tare da ƙwato kuɗaɗen da tura su zuwa inda ya dace domin amfanin ƴan Najeriya."

Tunji-Ojo Ya Magantu Kan Ganawarsa da Tinubu

A wani labarin kuma,.kun ji cewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya yi magana bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa.

Kiran da Tinubu ya yi wa ministan na zuwa ne bayan sunansa ya fito a badaƙalar kwangilolin da aka bayar a ma'aikatar jin ƙai ƙarƙashin Betta Edu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng