Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Sabon Harin Ta'addanci, Sun Kona Bayin Allah da Ransu a Borno
- Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon harin ta'addanci a garin Gajiram da ke ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar Borno
- A yayin harin ƴan ta'addan sun ƙona mutum shida ƙurmus har lahira tare da raunata wasu mutum huɗu
- Ƴan ta'addan dai sun kai harin ne bayan sallar Magriba a wata unguwa da kenkusa da kasuwar garin na Gajiram
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai sabon harin ta'addanci a garin Gajiram da ke ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar Borno.
Mutum shida ne suka ƙone ƙurmus yayin da wasu mutum huɗu suka samu raunuka daban-daban a harin da ƴan ta'addan suka kai da yammacin ranar Litinin, 8 ga watan Janairun 2024.
Majiyoyi waɗanda suka tabbatar wa jaridar Leadership harin ranar Talata a Maiduguri, babban birnin jihar, sun ce lamarin ya faru ne bayan sallar Magariba a wata unguwa da ke kusa da wata kasuwa a garin na Gajiram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa:
"An kashe mutum shida a jiya bayan sallar Magriba a Gajiram. Mutum huɗu sun samu raunuka. An kai harin ne a wata unguwa da ke kusa da kasuwar garin."
Rundunar soji da kuma rundunar ƴan sandan jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa dangane da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin fitar da wannan rahoton.
Bam ya tashi da matafiya a Borno
Rahoto ya zo cewa wasu matafiya mutum takwas sun rasa rayukansu bayan bam ya tashi da motocinsu suna tsaka da tafiya a jihar Borno.
Matafiyan dai na kan hanyarsu ne ta zuwa Dikwa daga Ngala lokacin da bam ɗin ya tashi da su. Mutane da dama sun samu munanan raunuka yayin da motocin suka yi lalacewar da ba za su gyaru ba.
Ƴan Boko Haram Sun Halaka Mutane a Chibok
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mayaƙan Boko Haram sun aikata ta'addanci a wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Chibok a jihar Borno.
Moyagun ƴan ta'addan na Boko Haram sun halaka mutum 12 tare da raunata wasu da dama a ƙauyukan Gatamarwa da Tsiha na ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng