Hankula Sun Tashi Bayan Yan Bindiga Sun Halaka Babban Basarake a Gidansa

Hankula Sun Tashi Bayan Yan Bindiga Sun Halaka Babban Basarake a Gidansa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun shiga har cikin gida sun halaka babban basarakem gargajiya a jihar Ogun
  • Moyagun ƴan bindigan da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar asiri ne sun halaka basaraken ne na ƙauyen Itunsokun a gidansa da ke Sagamu
  • Kisan basaraken ya sanya fargaba da tsoro a zuƙatan mutanen yankin inda ma'aikata suka yi gaggawar tashi daga ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Wasu ƴan bindiga sun kashe wani shahararren basaraken gargajiya, Adeyinka Folarin, Baasegun na ƙauyen Itunsokun a jihar Ogun.

Jaridar The Punch ta tattaro cewa ƴan bindigar da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne, a daren ranar Litinin da ƙarfe 8:00 na dare sun kai wa Folarin hari a gidansa da ke Sagamu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe basarake da wani manomi, sun tafka mummunar ɓarna a jihohin arewa 2

Yan bindiga sun halaka basarake a Ogun
Yan bindiga sun halaka babban basarake a Ogun Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ce wasu sarakunan gargajiya biyu da ba su son a bayyana sunayensu sun tabbatar da kisan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaya daga cikin sarakunan ya bayyana cewa:

"Eh da gaske ne amma ba ni da cikakken bayani game da lamarin. Mun ji cewa an kashe basaraken wanda shahararren basaraken gargajiya ne kuma mamba a majalisar sarakuna ta Akarigbo a daren jiya.
"Ana kiransa da sunan Baasegun, amma ba za mu iya cewa ga mutanen da suka aikata wannan mummunan aikin ba. Mun bar ƴan sanda da sauran jami’an tsaro su yi aikinsu."

Hankula sun tashi a Sagamu

Wani ma’aikacin ƙaramar hukumar Sagamu da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya sanya ma’aikatan ƙaramar hukumar suka yi gaggawar tashi daga aiki domin kada wani rikici ya ritsa da su.

Majiyar ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun yi luguden wuta kan yan ta'addan Boko Haram a Sambisa

"A yanzu da na ke magana da ku hankula sun tashi, inda ma'aikata suka fara ficewa daga sakatariyar ƙaramar hukumar domin gudun kada wani rikici ya ritsa da su.
"Mutane da yawa suna cewa ƴan ƙungiyar asiri ne suka kashe basaraken amma babu wanda zai iya tabbatar da hakan, har yanzu babu cikakken bayani."

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Omolola, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ƙara da cewa sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kutsa har cikin fada sun yi awon gaba da babban basarake a jihar Imo.

Ƴan bindigan dai sun sace Mai Martaba Eze Samuel Agunwa Ohiri, wanda shi ne sarkin Orodo a ƙaramar hukumar Mbatoili ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng