Gwamnatin Tarayya Za Ta Sayar da Kamfanin Lantarki Na Kaduna, an Bayyana Dalili
- Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin sayar da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KAEDCO)
- A cewar hukumar NERC, gwamnatin ta yanke wannan hukunci ne saboda bashin da ake bin kamfanin tsawon shekara biyu
- NERC ta ce tun da aka karbi hayar KAEDCO ba a samu wata riba ba, sai bashin naira biliyan 110 da ake bin sa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar kula da rarraba wutar lantarki ta Najeriya (NERC) za ta cefanar da kamfanin lantarki na Kaduna (KAEDCO) kan bashin sama da naira biliyan 110.
Bashin ta taru ne saboda shugabannin kamfanin sun gaza tafiyar da shi ta yadda za su sami riba tun bayan da suka karbi hayarsa shekaru biyu da suka wuce.
An gano dalilin cefanar da kamfanin KAEDCO
Daily Trust ta ruwaito cewa Najeriya na da kamfanonin raba wutar lantarki har guda 11 amma ba sa iya samun riba saboda karancin jari da haraji mai yawa da NERC ta kakaba masu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Litinin, hukumar NERC ta ce kamfanonin lantarki ciki har da NBET na bin kamfanin KAEDCO bashin sama da naira biliyan 110.
Da wannan hukumar ta yanke shawarar cefanar da kamfanin tare da ruguje shugabannin sa ta hanyar amfani da wata doka da aka samar 2023.
NERC ta nada sabon shugaban KAEDCO
Bankin Afrexim da Fidelity ne suka karbi hayar kamfanin KAEDCO a watan Yulin 2022 amma har yanzu babu batun samun riba a gudanarwa kamfanin.
NERC ta ce ta dora sabbin shugabannin kamfanin na wucin gadi har zuwa lokacin da za ta sayar da shi ga wanda ya fi taya wa da tsada.
Ta sanar da cewa Dr. Umar Abubakar Hashidu shi ne sabon shugaban kamfanin kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Kafin nada shi shugabancin KAEDCO, Mr Hashidu shi ne shugaban hukumar bunkasa shiyyar Arewa maso Gabas da kamfanin raba lantarki na Yola.
Wutar lantarki za ta wadaci ko ina a Najeriya - Ministan Tunubu
A wani labarin, gwamnatin Shugaba Tinubu ta ce kudirin dokar wutar lantarki na 2022 zai kawo karshen matsalolin da ake samu a rarraba wutar a Najeriya.
Gwamnatin ta ce akwai tsarin da za ta dauka wanda zai kawo karshen daukewar wutar lantarki a birane da karkara na fadin kasar.
Asali: Legit.ng