Kamfanin lantarki (KAEDCO) ya fadi dalilin raguwar samun wuta a Jihar Kebbi

Kamfanin lantarki (KAEDCO) ya fadi dalilin raguwar samun wuta a Jihar Kebbi

Biyo bayan zanga-zangar da wasu matasa suka gudanar a ranar Litinin 16 ga watan Satumba a Kebbi, dangane da tabarbarewar sha’anin lantarkin jihar. Kamfanin wutar lantarki wato KAEDCO yayi magana a kan lamarin.

Manajan kamfanin mai kula da shiyyar Kebbi, Dogara Saidu ya shaidawa manema labarai a hakikanin abinda ke faruwa ranar Talata a Birnin Kebbi.

KU KARANTA:Najeriya na kashe biliyan $1.2 duk shekara domin shigo da kifi – CBN

Manajan ya ce babu wani abu da ya sami wutar jihar Kebbi illa kawai abinda kamfanin ke fuskanta shi ne rashin biyan kudin wuta daga wurin jama’a.

Dogara ya ce: “A cikin watan Yuni mun sayi wuta mai yawan megawatt 33,978 a kan naira miliyan 853.8 inda abinda kawai muka iya samu a karshe watan shi ne naira miliyan 211.38 wanda ya ja mana hasarar naira miliyan 641.70.

Manajan ya kara da cewa a watan Yuli ma kwatankwacin abinda ya faru kenan, kamfanin asara yayi a maimakon ya ci riba. Wannan dalilin ne ya sanya ba za su cigaba da asara face su rage yawan wutar da suka saye domin tattalin ribarsu.

A bangaren gwamnatin jihar kuwa, kira tayi ga jama’a cewa su daure su rika biyan kudin wutansu a kan lokaci, domin bai wa gwamnati da kuma kamfanin damar biya masu bukatarsu kamar yadda ya kamata.

Jaridar Leadership ta tattaro mana cewa, gwamnatin jihar Kebbi ta ware kudi naira biliyan 1 domin bayar da na ta tallafi a bangaren samar da wutar lantarkin. Haka kuma ta sanya na’urorin samar da lantarkin wato taransfoma domin tabbatar da an samu wuta tsawon awa 24 a ko wace rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel