Shinkafar Naira Biliyan 57 da Tinubu Ya Raba Ya Tona Asirin Sanatoci, ‘Yan Majalisa

Shinkafar Naira Biliyan 57 da Tinubu Ya Raba Ya Tona Asirin Sanatoci, ‘Yan Majalisa

  • Fadar shugaban kasa ta hada-kai da ‘yan majalisa domin ayi wa jama’a rabon kayan abinci a mazabu
  • Bola Ahmed Tinubu ya umarci ma’aikatar gona ta bada shinkafa ga Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai
  • Wasu ‘yan majalisar sun raba buhunan shinkafa, a wasu garuruwan kuwa talakawa ba su san ana yi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ana ta surutu a game da shinkafar N57.8bn da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni a rabawa talakawa a mazabunsu.

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni a raba shinkafa ta hannun ‘yan majalisu.

Bola Tinubu ya raba shinkafa
Bola Tinubu ya rabawa 'yan majalisa shinkafa Hoto: @Dolusegun16, @thesunnigeria
Asali: Twitter

Wasu ‘yan majalisar sun tabbatar da cewa sun karbi kayan abinci, wasu sun nuna ba su da masaniya a game da tallafin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa sun sake ware wani Naira Biliyan 30 domin gyare-gyaren ginin Majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tallafin buhunan shinkafan N57bn

Fadar shugaban kasa ta jero rabon shinkafar a cikin nasarorin da Bola Tinubu ya samu da aka yi waje da tsarin biyan tallafin fetur.

Bayanan da aka fitar ya ce an warewa duk Sanata kayan tallafin N200m yayin da ‘yan majalisar wakilan tarayya su ka tashi da N100m.

Idan aka yi lissafi, gwamnatin Bola Tinubu ta kashe N57.8bn a wajen bada tallafi ta hannun Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai fiye da 460.

Yadda aka raba shinkafa a majalisa

Bayo Onanuga ya tabbatar da haka, ya ce shugaban kasa ya umarni ma’aikatar gona ta bada kayan abincin ne ga ‘yan majalisar ne a raba.

Akasin tunanin da wasu su ke yi, ba kudin aka ba ‘yan siyasar ba, sai abinci na darajarsu kamar yadda Segun Dada ya tabbatar a shafin X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya umarci a yi bincike kan kudin tallafin talakawa N37bn da aka sace a ofishin Betta Edu

Rahoton ya ce ganin an ba gwamnoni kayan abinci ne sai ‘yan majalisa su ka huro wuta, yanzu sai ga shi ana zargin sun boye buhunan.

‘Yan majalisar sun rika kamun kafa a fadar shugaban kasa domin samun kayan tallafin da aka amince da kwarya-kwarya kasafin 2023.

Da yake rabon buhuna 2, 400 a Edo, Dekeri Anamero mai wakiltar Etsako a majalisa ya ce shugaba Bola Tinubu ya ba su motocin shinkafa.

Gyare-gyaren N30bn a Majalisa

Rahoton da aka fitar a safiyar Litinin ya nuna gyare-gyare da ‘yan kwaskwarima a nan da can za su ci Naira Biliyan 60 a majalisar tarayya.

A kasafin da aka yi a 2024, ‘yan majalisar tarayya sun kuma cusa kudin yin gyara dDuk da Muhammadu Buhari ya ware kudin gyara a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng