Dakarun Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta Kan Yan Ta'addan Boko Haram a Sambisa

Dakarun Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta Kan Yan Ta'addan Boko Haram a Sambisa

  • Ƴan ta'addan Boko Haram sun sheƙa barzahu bayan dakarun sojojin sama sun yi musu luguden wuta
  • Dakarun sojojin na Operation Hadin Kai sun halaka ƴan ta'adda 12 a farmakin da suka kai musu kusa da dajin Sambisa
  • Farmakin dai ya biyo bayan hango miyagun ƴan ta'addan da aka yi suna jigilar kayayyaki waɗanda aka kyautata zaton makamai ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta’adda da dama a wani samame da suka kai tsakanin ranakun 2 zuwa 6 ga watan Janairu a yankuna daban-daban na jihar Borno.

A yayin farmakin da aka kai a kusa da dajin Sambisa, an hango ƴan ta’addan suna ta jigilar wasu abubuwa da ake zargin makamai da alburusai ne zuwa yankin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara binciken minista kan badakalar N585.2m

Sojojin sama sun sheke yan ta'addan Boko Haram
Dakarun sojojin sama sun halaka mayakan Boko Haram a Borno Hoto: @NigAirForce
Asali: Facebook

Sanarwar da daraktan hulɗa da jama’a da yada labarai na rundunar sojan sama ta Najeriya, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa an jefa bama-bamai kan ƴan ta’addan da makamansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gabkwet ya bayyana cewa an kashe ƴan ta’adda 12 a yayin farmakin, rahoton jatidar Leadership ya tabbatar.

Yadda aka kai farmaki kan ƴan ta'addan

A kalamansa:

“Haɗuwar da ƴan ta’addan suka yi a wurin ya sanya ana zargin aniyarsu da shirinsu, don haka aka ba da umarnin kai farmaki wurin.
"Sakamakon harin ya haifar da wata babbar gobara daga wurare biyu da ke wajen, yayin da aka ga wasu ƴan ta'adda da suka tsira suna arcewa domin tsira da rayukansu."

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, an kashe ƴan ta'adda 12 a harin, kuma an lalata musu kayan aikinsu, wanda hakan ya lalata ƙarfinsu na kai hari a ƙananan wurare da kan sojoji.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya yi Allah wadai da hare-haren yan bindiga, ya sha muhimmin alwashi

Gabkwet ya kuma ce bayan rahoton sirri da aka samu, sojojin sun gudanar da wani samame a yankin tafkin Chadi, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ƴan ta’adda tare da lalata motocinsu da babura.

Dakarun Sojoji Sun Sheƙe Ƙasurgumin Ɗan Ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama sun samu nasarar sheƙe ƙasurgumin ɗan ta'adda, Yellow Jambros.

Sojojin sun sheƙe ƙasurgumin ɗan ta'addan ne tare da mayaƙansa lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Neja daga Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng