Badakalar N585m: Fadar Shugaban Kasa Ta Janye Katin Betta Na Shiga Villa, An Hana Ta Ganin Tinubu

Badakalar N585m: Fadar Shugaban Kasa Ta Janye Katin Betta Na Shiga Villa, An Hana Ta Ganin Tinubu

  • Ministar da aka dakatar, Dr Betta Edu, na fuskantar tarin kalubae yayin da fadar shugaban kasa ta dauki mataki kan zargin tafka badakalar kudi
  • Wata majiya abun dogaro ta bayyana cewa an janye katinta na shiga fadar shugaban kasa wanda shine ke bata damar ganin Shugaban kasa Tinubu
  • Wannan matakin ya biyo bayan binciken da ake gudanarwa kan yadda ministar ta tafiyar da harkokin ma'aikatarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fadar shugaban kasa, Abuja - Ana ci gaba da fafatawa yayin da fadar shugaban kasa ta janye katin dakatacciyar ministar jin kai da kawar da talauci, Dr Betta Edu, wanda hakan zai hana ta shiga fadar villa da ke Abuja.

An hana Betta Edu damar ganin Tinubu
Badakalar N585m: Fadar Shugaban Kasa Ta Janye Katin Betta Na Shiga Villa, An Hana Ta Ganin Tinubu Hoto: Dr Betta Edu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ku tuna cewa Tinubu ya dakatar da Edu daga kujerarta a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu. kakain shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya ce ci gaban ya yi daidai da alkawarin da ya dauka na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da arzikin yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani yayin da Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ya yi shagube ga Buhari

Awanni bayan dakatar da ita, fadar shugaban kasa ta toshe kafar da Edu za ta gana da Shugaban kasa Tinubu a Villa, rahoton Nigerian Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake martani, kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale, wanda aka yi wa tambayoyi a kafar yada labarai, ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar gaskiya da amana kan umurnin da Tinubu ya ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Dalilin janye katin Edu na shiga Villa

Sai dai kuma, katin na ba manyan jami'an gwamnati damar shiga fadar shugaban kasa domin ganawa da Shugaban kasa Tinubu.

Da take magana kan ci gaban, wata majiya abun dogaro a fadar shugaban kasar ta fada ma jaridar Daily Trust cewa:

"An karbi katin dakatacciyar minista na shiga fadar Villa."
"Wannan yana nufin yanzu ba za ta iya shiga Villa ba har sai an bayar da umurni na gaba," majiyar ta kara da cewa.

Kara karanta wannan

Awanni kadan bayan dakatar da ita, Ministar Tinubu ta sha kunya a fadar Aso Rock, an fadi dalili

Betta Edu za ta fuskanci EFCC

A baya mun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni ga hukumar EFCC ta yi cikakken bincike a ma’aikatar jin kai da yaki da talauci.

Shugaban kasar ya sanar da haka ne a jawabin da Ajuri Ngelale ya fitar yayin da aka dakatar da Betta Edu game da zargin badakalar N585m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng