Jerin Mutanen da Buhari Ya Nada Mukamai da Tinubu Ke Bincika Ta Hanyar Amfani da EFCC
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara bincikar wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
- Daga cikin waɗanda ake bincike akwai tsohon gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, wanda ya samu beli kwanan nan
- Emefiele dai yana fuskantar tuhume-tuhume da dama kan yadda ya tafiyar da babban bankin na CBN
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ba kawai korar wasu daga cikin waɗanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa ya yi ba, amma ya fara binciken wasu daga cikinsu ta hanyar amfani da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC).
Ana binciken wasu tsofaffin ƴan majalisar ministocin tsohon shugaban ƙasa Buhari da laifin karkatar da kuɗaɗen gwamnati.
Ga jerin su kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Godwin Emefiele
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya kasance tsohon shugaban kasa Buhari ne ya naɗa shi a ƙarshen wa'adin naɗin da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya yi masa.
Sai dai kuma shugaba Tinubu ya dakatar da shi jim kadan bayan ya shiga ofis.
Bayan dakatar da shi daga aiki, EFCC ta kama Emefiele, kuma kwanan nan wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belinsa kan Naira miliyan 300.
Sai dai, duk da bayar da belin Emefiele, taƙaddamarsa ba ta ƙare ba, domin Jim Jim Obazee, wani mai bincike na musamman da shugaba Tinubu ya naɗa domin ya binciki ayyukan bankin a tsawon wa’adin da Emefiele yake a ofis, ya bankaɗo wasu laifukansa.
Obazee ya gabatar da tuhume-tuhume da dama a kan tsohon gwamnan na CBN.
A wani al’amari na baya-bayan nan, hukumar EFCC ta samu Emefiele da laifi a bisa binciken da ta ke yi na yin almundahana kan canjin kuɗi a cikin shekara tara da suka gabata a CBN.
Sadiya Umar-Farouk
Sadiya Umar-Farouk ta riƙe muƙamin ministan harkokin jin ƙai, a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023, a wa’adi na biyu na mulkin tsohon shugaban ƙasa Buhari.
Ana tuhumar ta ne a wani bincike da ake yi kan N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar da ita a lokacin da take riƙe da muƙamin minista.
Alƙali Ya Tura Emefiele Gidan Gyaran Hali
A wani labarin kuma, kun ji cewa alƙalin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ya tura Godwin Emefiele, zuwa gidan gyaran hali na Kuje.
Alƙalin kotun ya tura Emefiele zuwa gidan gyaran halin ne har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan belinsa.
Asali: Legit.ng