NSIPA Ta Fallasa Gaskiya Kan Ministar Tinubu da Ake Zargi da Hannu a Badakar Kudin Talakawa
- Hukumar jin dadin al'umma ta kasa (NSIPA) ta yi watsi da badakalar kudi da aka yi wa ministar jin kai, Betta Edu
- Shugaban sashin sadarwa na NSIPA, Jamaludeen Kabir, ya nesanta hukumar daga zargin da ke alakanta Edu da badakalar NSIPA
- Kabir ya kara da cewa ministar ba ta da hannu a duk wani hada-hadar kudi ko yanke hukunci a hukumar NSIPA
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Hukumar jin dadin al'umma ta kasa (NSIPA) ta yi martani kan zargin badakalar kudi da ake yi wa ministar jin kai da kawar da talauci, Betta Edu.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, manajan labarai na NSIPA, Jamaludeen Kabir, ya yi watsi da ikirarin da ke alakanta ministar da badakalar kudi a hukumar.
Kabir ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 6 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda sanarwar ta nuna, Edu ba ta da hannu a duk wani hada-hadar kudi ko yanke hukunci a hukumar NSIPA wacce ke karkashin bincike a halin yanzu.
“NSIPA ta nisanta kanta daga duk wani ikirarin da ke alakanta mai girma Minista da badakalar kudi ko kuma wani laifi a cikin hukumar.
“Yana da matukar muhimmanci a jaddada cewa mai girma Minista ba ta da hannu a duk wani hada-hadar kudi ko yanke shawara a NSIPA wacce ke karkashin bincike a yanzu."
Betta Edu ta magantu kan badakalar 3bn
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, Dr Betta Edu, ta ce ba ta da alaƙa da almundahanar Naira biliyan 3 da aka yi a hukumar jindaɗin al'umma ta ƙasa (NSIPA).
Edu ta bayyana sanya ta a cikin almundahanar N30bn a matsayin ƙarya wacce kuma ba ta da tushe ballantana makama.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu mai taken “Betta Edu na da alaƙa da badakalar zamba ta N3bn a NSIPA; zarge-zarge marasa tushe da nufin karkatar da hankalin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa."
Asali: Legit.ng