Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dan Haya Da Ya Lakadawa Mai Gida Dukan Kawo Wuka

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dan Haya Da Ya Lakadawa Mai Gida Dukan Kawo Wuka

  • Wata kotu mai daraja ta daya a Abuja, ta garkame wani Mr Okeye kan zargin ya hada kai da 'yayansa sun lakadawa Mr Isaac dukan tsiya
  • Mr Isaac shi ne mamallakin gidan da Mr Okeye ya ke haya a ciki, kuma ya shigar da Okeye kara gaban 'yan sanda kwana biyu da suka wuce
  • Jami'in da ya shigar da karar ya shaidawa kotun cewa 'yayan Mr Okeye da wani Gideon da suka aikata laifin tare sun tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Juma’ar da ta gabata, kotun AKabusa mai daraja ta daya da ke Abuja ta ba da umarnin tsare wani dan haya mai suna Chris Okoye bisa laifin dukan mai gidan da ya ke haya a ciki.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan sanda sun kama magidanci kan ‘dabawa’ matarsa wuka a Yobe

Mai shari'a, Malam Abubakar Sadiq ne ya bayar da umurnin tsare mutumin bayan jin ta bakin bangarorin biyu.

Kotu ta kulle dan haya da ya lakadawa mai gida duka a Abuja
Kotu ta garkame Chris Okoye bisa laifin dukan mai gidan da ya ke haya a ciki a Abuja. Hoto: Babbar Kotun Tarayya
Asali: UGC

Wanda ake karar ya ce bai aikata laifin komai ba

Ana tuhumar wanda ake karar da ke zama a gida mai lamba '2A Niger Avenue villa nova', garin Apo, da aikata lafin barazana, amfani da karfi, cin zarafi da yi wa mutum lahani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, wanda ake karar ya ce sam bai aikata dukkanin wadannan laifuka da ake zargina da aikata wa ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jami'in da ya shigar da karar, O.S Osho ya shaida wa kotun cewa mai gidan, Mr Ochengele Isaac, ya shigar da kara gaban hukumar 'yan sandan Apo a ranar 3 ga watan Janairu.

'Yayan Mr Okeye da kuma Gideon sun tsere

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta kori jami'anta 2 daga aiki, za ta gurfanar da su gaban kotu, ta fadi dalili

Ya ce wanda ake karar da 'yayansa biyu da wani Gideon wanda ya tsere, suka taru sun lakadawa mai gidan dukan kawo wuka har suka ji masa raunuka.

Tribune Online ta ruwaito cewa Osho ya sanar wa mai shari'ar kotun cewa 'yayan Okeye da kuma Gideon sun tsere bayan aikata laifin, amma 'yan sanda na kan neman su.

Mai shari'a Sadiq ya dage zaman sauraron shari'ar har sai zuwa ranar 16 ga watan Janairu za a ci gaba.

Rundunar 'yan sanda ta kori jami'anta biyu daga aiki a Legas

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta sallami jami'anta guda biyu daga aiki, bisa kama su da laifukan fashi da makami a jihohin Legas da Ogun, kuma za a gurfanar da su gaban kotu.

Rahotanni sun nuna cewa Sufeta Sunday Adetoye da Sufeta Ogunleye Stephen na aiki a hedkwatar rundunar shirya ta 2, da ke Onika, jihar Legas, kafin a kore su daga aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel