Kano: Ana Daf da Yanke Hukuncin Zaben Jihar, Rundunar 'Yan Sanda Ta Samu Wata Gagarumar Nasara

Kano: Ana Daf da Yanke Hukuncin Zaben Jihar, Rundunar 'Yan Sanda Ta Samu Wata Gagarumar Nasara

  • Yayin da ke dakon hukuncin Kotun Koli, rundunar 'yan sanda a Kano ta yi wata ganawa da 'yan daba a jihar
  • Rundunar ta yi gayyatar ce da 'yan yankin Kwanan Dangora da ke karamar hukumar Kiru don tattaunawa da matasan
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 6 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta gayyaci kasurguman 'yan daba 52 don tattaunawa.

Rundunar ta ce ta yi gayyatar ce a yankin Kwanan Dangora da ke karamar hukumar Kiru don samun maslaha, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

'Yan sanda sun aiwatar da wani babban aiki a Kano yayin da ake dakon hukuncin shari'ar zabe
Rundunar 'yan sanda a Kano ta yi wata ganawa da 'yan daba 52 a jihar. Hoto: Abba Kabir, NPF.
Asali: Facebook

Wane roko rundunar ta yi ga jama'ar Kano?

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 6 ga watan Janairu a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiyawa ya ce kwamishinan 'yan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya roki masu ruwa da tsaki da su taimaka wa rundunar wurin tabbatar da zaman lafiya.

Gumel ya kuma roki mazauna yankin Kwanan Dangora da su zakulo 'yan dabar da ke rayuwa a wurin don daukar mataki, cewar Pulse.

Sakon rundunar ta tura ga masu ruwa da tsaki

Ya ce a yanzu haka an samu 'yan dabar akalla 52 da suke ingiza wutar rashin zaman lafiya a yankin.

Kiyawa ya ce bayan ganawa da 'yan dabar, kwamishinan ya jagoranci jami'an 'yan sanda zuwa kan hanyar Kano zuwa Kaduna don gane wa idonsa yanayin tsaro.

Kara karanta wannan

Tashin hankali bayan tirela ta murkushe sabon dan sanda a bakin aiki a jihar Arewa, bayanai sun fito

Kwamishinan ya godewa shugaban laramar hukumar da kuma masu rike da masarautun gargajiya kan kokarin da suke yi wurin kawo zaman lafiya.

An kama matashi da zargin soka wa limamin wuka a Kano

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta cafke wani matashi da zargin hallaka limamin masallacin Unguwansu.

Ana zargin matashin da soka wa limamin wuka bayan ya yi kokarin hana shi yayin da ya ke shan tabar wiwi a kusa da masallacin.

Hakan ya biyo bayan kama wani matashi likitan bogi da ya yi ajalin wata budurwa da niyyar zubar mata da ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.