Dangote Ya Kara Shiga Matsala Bayan Hukumar EFCC Ta Ba Shi Sabon Umarni
- Hukumr EFCC na cigaba da gudanar da bincike kan badakalar aikata ba daidai ba wajen bayar da kuɗaɗen canji
- Binciken ya kai kan kamfanin Dangote wanda jami'an hukumar ta EFCC suka dira a birnin Legas
- Bayan kai samame a babban ofishin na Dangote, jami'an na EFCC sun umarni manyan jami'an kamfanin da su zo Abuja da wasu takardu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati (EFCC) ta gayyaci wasu jami’an kamfanin Dangote zuwa Abuja domin su zo da cikakkun takardu kan hada-hadar kuɗaɗen canji da kamfanin ya yi a cikin shekara tara da suka gabata.
A ranar Alhamis ne jami’an EFCC suka kai samame hedikwatar kamfanin Dangote da ke Ikoyi a Legas, a cigaba da bincike kan zargin cin hanci da rashawa da wajen bayar da kuɗin canji da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi.
Hukumar EFCC na binciken zargin bada fifiko ga rukunin Dangote mallakin hamshakin attajirin nan Aliko Dangote da wasu kamfanoni 51 da CBN ya yi ƙarkashin jagorancin Emefiele, cewar rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa a ranar Juma’a jami’an EFCC suka kwashe wasu takardu daga babban ofishin kamfanin a ranar Alhamis, amma ba su ƙunshi dukkanin hada-hadar da aka yi ba, domin haka suka yanke shawarar kiran jami’an da su kawo takardun zuwa Abuja ranar Talata.
Me hukumar EFCC take buƙata?
Sai dai wani babban jami’in hukumar ta EFCC wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an ba manyan jami’an kamfanin wa’adin ba hukumar abin da ya kira “cikakkun takardun bayanai kan buƙatun hukumar.
An tattaro cewa ana sa ran jami'an a ofishin hukumar a ranar Talata.
A kalamansa:
"Eh, (jami’an Dangote) sun nemi a ba su lokaci domin su samu duk wasu takardun da ake bukata, shi ne aka ba su. Abin da ake so shi ne ba a so a ga kamar ana farautar wani. Abin da hukumar ke so shi ne ta samu shaidu da cikakkun bayanai kan yadda aka raba kuɗaɗen gwamnati shi ne kawai."
Wani jami’in kamfanin Dangote ya kuma tabbatar da cewa a halin yanzu wasu manyan ma’aikatan kamfanin na tattara takardun da hukumar EFCC ta buƙata a wanke kamfanin daga aikata ba daidai ba.
Sadiya Farouk Ta Bayyana Dalilin Ƙin Bayyana Gaban EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohuwar ministar jin ƙai da walwalar jama'a, Sadiya Umar Farouk ta bayyana dalilin kin amsa gayyatar hukumar EFCC kan badaƙalar kuɗaɗe.
Hukumar na zargin Ministar Buhari ne da karkatar da naira biliyan 37 na ma'aikatarta yayin da ta ke Minista.
Asali: Legit.ng