Dalilin da Yasa Ya Kamata Mata Su Rika Shiga Aikin Soja, Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf

Dalilin da Yasa Ya Kamata Mata Su Rika Shiga Aikin Soja, Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kwadaitar da mata a kan su shiga aikin soja
  • Gwamna Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda ake barin mata a baya musamman a bangarorin tsaro
  • Ya kuma sha alwashin wayar masu da kai kan muhimmancin shiga irin wannan aikin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bukaci mata da su shiga aikin soja, musamman ma na sojan kasa.

Gwamnan ya magantu ne yayin da yake nuna rashin jin dadinsa kan yadda babu isassun mata a wajen shirin tantance yan jihar Kano masu son shiga aikin sojan Najeriya, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi dabara 1 da ta dauko domin karya farashin abinci a 2024

Abba Kabir Yusuf ya nunawa mata muhimmancin shiga aikin soja
Dalilin da Yasa Ya Kamata Mata Su Rika Shiga Aikin Soja, Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Yusuf ya bayyana haka ne ta bakin kwamishiniyarsa ta ayyuka na musamman, Hajiya Amina Abdullahi, wacce ta sanya ido kan yadda aka gudanar da shirin a barikin Bukavu da ke cikin babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma sha alwashin yin amfani da dukkan hanyoyin da ake da su wajen fadakar da mata a fadin lungu da sako na jihar kan mahimmancin shiga irin wannan aikin.

An bar mata a baya wajen ayyukan tsaro, Gwamna Abba Yusuf

A cewar gwamnan, mata sun zama kashin baya a abubuwa da dama a kasar nan, musamman ma a fannin ayyukan tsaro.

Kimanin matasa 150 ne suka samu nasarar cin tantancewar, kuma gwamnan ya bukace su da su jajirce wajen fuskantar kalubalen da ke gabansu, inda ya ba su tabbacin cewa na dan lokaci ne kawai.

Ya bayyana cewa, a matsayinsa na gwamnan jihar, zai yi iya kokarinsa wajen tallafa musu ta kowace hanya da za su kai ga cimma burinsu, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rantsar da sabbin ciyamomi 38 da mataimakansu, sun kama aiki gadan-gadan

Yusuf, wanda ya sha alwashin yin amfani da nagartaccen ofishinsa wajen tabbatar da ganin wadanda ba su cika sharuddan da ake bukata ba a yayin atisayen sun yi haka, ya kuma umarci wadanda suka cancanta da su kare martabar jihar.

Ya ce hakan ya zama dole domin a cewarsa Kano ce kan gaba a kodayaushe yayin da saura ke bin sahunta.

Legit Hausa ta tattauna da wasu matan arewa don jin dalilin da yasa basa son shiga aikin soja inda duk suka alakanta abun da al’ada.

Malama Rahama Sa’id ta ce:

“Ba kin aikin soja muke ba amma a al’adar mallam Bahaushe ba kasafai iyaye za su bar diyarsu mace ta shiga aikin ba koda kuwa tana matukar son aikin. Kawai mu mun dauki aikin soja a matsayin na maza ne don haka ne da wuya kiga yarinya tace maki za ta yi soja.”

Malama Zahra kuwa cewa ta yi:

Kara karanta wannan

Bayin Allah sama da 100 sun mutu yayin da bama-bamai suka tashi a wurin taro kusa da Masallaci

“Ke kuwa wani dan farin hula a arewa ne zai auri macen soja, abun da kamar wuya. Ko shi yana so yan uwa da danginsa za su yi surutu ba kadan ba. Cewa za a yi zaman aure za ta yi ko zuwa yaki.”

Sojoji sun kashe shugaban yan ta'adda

A wani labarin kuma, mun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe shugaban ƙungiyar ta'addanci ISWAP, Ba'a Shuwa, da gomman mayaƙansa a jihar Borno.

Sojojin sun halaka ƙasurgumin ɗan ta'addan ne yayin wani liguden wuta da suka yi a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ranar 2 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng