Mayakan Boko Haram Sun Yi Ajalin Babban Malamin Addini a Yobe Bayan Hallaka Wasu Mutane 5

Mayakan Boko Haram Sun Yi Ajalin Babban Malamin Addini a Yobe Bayan Hallaka Wasu Mutane 5

  • Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun yi ajalin wani babban Fasto a jihar Yobe a daren Juma'a
  • Fasto Luka Levong ya gamu da ajalinsa ne bayan mayakan sun kai hari a garin Kwari da ke karamar hukumar Geidam a jihar Yobe
  • Wata majiya ta tabbatar cewa mayakan sun kai harin ne da misalin karfe 2 na daren yau Juma'a 5 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe - 'Yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun hallaka wani Fasto a jihar Yobe.

Marigayin mai suna Luka Levong ya gamu da ajalinsa ne bayan harin na su a garin Kwari da ke karamar hukumar Geidam a jihar.

Kara karanta wannan

An kama wata ‘kwararriyar’ barauniyar waya da wasu mutum 84 a Borno, ta bayyana yadda ta ke takunta

Boko Haram sun hallaka malamin addini a Yobe
Boko Haram sun yi ajalin wani fitaccen Fasto a Yobe. Hoto: Nigeria Army.
Asali: Twitter

Yaushe mayakan suka kai hari a Yobe?

Har ila yau, mayakan sun hallaka wasu mutane biyar yayin mummunan harin da suka kai a garin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna garin sun tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa mayakan sun kai harin ne da misalin karfe 2 na daren yau Juma'a 5 ga watan Janairu.

Majiyar ta ce an hallaka Faston da kuma ma'ajin cocinsa mai suna Maina Abdullahi kafin zuwan jami'an tsaro.

Wane martani soji da 'yan sanda suka yi?

Ta ce mayakan sun kuma kai wasu hare-hare daban inda suka yi ajalin wasu mutane da kuma cinna wa cocin da wasu gidaje wuta a yankin.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto jami'an 'yan sanda da na sojoji ba su yi martani ka na harin ba.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan mayakan Boko Haram sun kai hari a wani kauye inda suka hallaka mutane 12.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Jerin malamai 2 da suka hangowa kiristoci matsala a 2024

'Yan sanda sun cafke kwararriyar mai satar waya

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta cafke wata mata da ta kware wurin satar wayar jama'a a Maiduguri.

Wacce ake zargin mai suna Fatima Abacha da aka fi sani da 'Bintu' ta shiga hannun 'yan sanda a ranar 28 ga watan Disamba.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Daso Nahum ya tabbatar da kama matar inda ya ce sun cafke wasu mutane 84 kan zarge-zarge.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.