Daliban Najeriya 15, 000 Sun Yi Carko-Carko da Aka Dakatar da Karbar Digirin Benin

Daliban Najeriya 15, 000 Sun Yi Carko-Carko da Aka Dakatar da Karbar Digirin Benin

  • Kungiyar dalibai ta NANS ta yabi gwamnatin tarayya a kan matakin da ta dauka na bincike a kan digirin bogi
  • Shugaban NANS na reshen kasar Benin ya ce akwai daliban da su ke karatu bisa ka’ida a jami’o’in na waje
  • Ugochukwu Favour yana so gwamnati ta bambance tsakanin daliban kwarai da masu neman shaidar digirin zir

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kungiyar NANS ta reshen daliban Najeriya da ke Benin ta ce akwai mutanen kasar nan da-dama da su ke karatun digiri a makwabta.

Shugaban NANS na reshen kasar Benin, Ugochukwu Favour ya yi hira da Channels a kan dakatar da digirin wasu kasashe da aka yi.

Daliban Najeriya a waje
Wani dalibin Najeriya a jami'ar waje Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kwamred Ugochukwu Favour ya ce dalibai akalla 15, 000 ake da su daga Najeriya da su ka tafi neman ilmin zamani a kasar Benin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kara dakatar da karbar digiri daga wasu kasashe bayan Benin da Togo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tsaida karbar digirin wasu kasashe

Gwamnatin tarayya ta dakatar da karbar takardar shaidar karatu daga jami’o’in Benin, Togo, Uganda da wasu kasashe a Afrika.

Hakan ya zama dole ne bayan wani ‘dan jarida ya bankado badakalar da ake tafkawa da sunan karatun digiri a wadannan jami’o’i.

Abin zai shafi digirin mutane 15, 000

Shugaban kungiyar daliban ya bada shawara gwamnati ta yi la’akari da halatattun dalibai da ke karatu ba tare da sabawa ka’ida ba.

Da aka yi hira da Ugochukwu Favour, ya nuna goyon baya a kan matakin da aka dauka kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Shugaban daliban ya ce akwai bukatar a hukunta duk wanda aka samu da laifi wajen bada digirin bogi a jami’o’in kasahen ketaren.

NANS da binciken Digirin Benin

Daily Trust ta rahoto Favour yana cewa tuni kungiyar NANS ta kasar Benin ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki lamarin.

Kara karanta wannan

Bayan dan jarida ya yi fallasa, FG ta dakatar da ‘karbar’ digiri daga Togo da Jamhuriyar Benin

Dalibin yana fatan sakamakon bincikensu zai yi amfani domin hana aukuwar haka a gaba.

Sai dai Kwamred Favour ya ce bai kamata gwamnatin Najeriya tayi wa kowa kudin goro saboda laifin da wasu daidaiku su ka aikata ba.

Idan aka yi hukunci a kan kowa, shugaban kungiyar daliban ya ce a Benin kurum abin zai shafi ‘yan Najeriya kusan 15, 000 da ke karatu.

Za a samu karin jami'o'i a Najeriya?

Gwamnatin tarayya ta na fama da malaman jami’a na kungiyar ASUU, sai ga labari ana shirin hada ta da karin wasu jami’o’i a Najeriya.

Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai sun kawo kudirorinsu domin a kirkiro da sababbin makarantun gwamnatin tarayya a mazabunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng