An kwashe shekaru 6 kenan babu bullar cutar shan-ina a Jigawa

An kwashe shekaru 6 kenan babu bullar cutar shan-ina a Jigawa

- Gwamnatin jihar Jigawa ta ce jihar bata samu bullar cutar shan inna ba cikin shekaru shida da suka wuce

- Sakataren hukumar lafiya kula da lafiya mataki na farko a jihar, Dr Kabir Ibrahim ya daganta nasarar ga gudunmawa da Sarakunan gargijiya da shugabanin addini suka bayar

- Dacta Ibrahim kuma ya yi kira ga iyayen yara da su rika bayar da yaran su domin ayi musu rigakafin

Babban Sakataren hukumar samar da lafiya mataki na farko a jihar Jigawa (JSPHDA) ya ce ba'a samu bullar cutar shan inna a jihar ba har na tsawon shekaru 6 da suka wuce. Ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da kamfanin dillanci labarai (NAN) ranar Alhamis a garin Dutse.

Ya ce an samu nasarar fatatakar cutar na jihar ne saboda gudunmawa da masu sarautun gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a fanin suka bayar a jihar.

Labari mai dadi: Ba'a samu bullar cutar shan ina ba cikin shekaru shida da suka shude a Jigawa
Labari mai dadi: Ba'a samu bullar cutar shan ina ba cikin shekaru shida da suka shude a Jigawa

DUBA WANNAN: Bamu da lokaci, ku gaggauta sakin kasafin kudin bana - Fadar shugaban kasa ta fadawa 'yan majalisa

Duk da haka, jami'in lafiyar ya koka ga halin ko in kula da wasu iyaye ku nuna wa wajen kai yaran su wajen rigakafin. Ya ce rigafin asali a asbiti a keyi amma yanzu ana bin mutane kauyuka ana rokon su kafin su bayar da yaran su ayi musu rigakafin.

Ya kara da cewa hukumar lafiyar tare da hadin gwiwar wasu masu ruwa da tsaki suna iya kokarin su wajen wayar da kan al'umma kan muhimmancin rigakafin.

Ibrahim ya mika godiyar sa ga shuwagabanin addini, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudunmawar su kan muhimmancin rigafin shan innan da na sauran cututuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164