“Kai Jan Gwarzo Ne”, Tinubu Ya Yi Ruwan Kalaman Yabo Ga Gwamna Yusuf Na Jihar Kano, an Gano Dalili
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sha ruwan yabo daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Shugaba Tinubu ya yi kalaman ne a yayin da ya ke taya Gwamna Abba murnar cika shekara 61 da haihuwa
- Sanarwar da Chief Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis a madadin Tinubu, ta nuna irin namijin kokarin Gwamna Yusuf
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Shugaban kasar Najeriya, mai girma Bola Tinubu ya taya gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwa a shafinta na Twitter (X), Tinubu ya taya Abba murnar cika shekara 61 da haihuwa.
Takaitaccen tarihin Gwamna Yusuf
Wani rahoto da shafin Wikipedia ya fitar, ya nuna cewa an haifi Abba Kabir Yusuf a ranar 5 ga watan Janairu, 1963 a karamar hukumar Gaya, jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An haifi Gwamna Yusuf a zuriyar Sullubawa Fulani. Sunan mahaifinsa Malam Kabiru Yusuf, sunan mahaifiyarsa Malama Khadijatul-Naja'atu.
Kakan sa Alhaji Yusuf Bashari shi ne Hakimin Gaya na wancan lokacin, kuma a wajen sa ne Yusuf ya yi karatun addini.
Shugaba Tinubu ya jinjina wa Abba Gida-Gida
A cewar sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar:
"Shugaba Tinubu ya jinjina namijin kokarin Gwamna Yusuf, na yadda ya yi gwagwarmaya daga hadimi, zuwa kwamishina, zuwa gwamnan jiha.
"Shugaban kasar na yi wa gwamnan fatan alkairi a yayin da ya ke gudanar da ayyukan sa."
Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Chief Ajuri Ngelale ta ce shugaba Tinubu ya kuma yi addu'ar gwamnan ya yi shekaru masu albarka nan gaba.
Yan bindiga sun harbe limamin masallaci har lahira a Amurka
A wani labarin, wasu 'yan bindiga sun harbe limamin masallaci a Newark, da ke a jihar New Jersey, kasar Amurka, inda ya mutu bayan a asibiti.
Antoni janar na jihar, Matt Platkin ya sanar da rasuwar Hassan Sharif, tare da shan alwashin gano wadanda suka yi kisan don hukunta su.
Asali: Legit.ng