Rundunar ’Yan Sanda Ta Kori Jami’anta 2 Daga Aiki, Za Ta Gurfanar da Su Gaban Kotu, Ta Fadi Dalili
- Rundunar 'yan sanda ta sallami wasu jami'anta guda biyu tare da shirin gurfanar da su gaban kotu
- Rundunar ta kama jami'an tare da wasu mutum uku daga kungiyar 'yan bijilante bisa laifin fashi da makami a jihar Ogun
- Rahotanni sun bayyana cewa, wani ASP Ajaiyi Victor da ya jagoranci fashin ya tsere, ana nemansa ruwa a jallo
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Legas - Rundunar 'yan sanda ta kori sufeta Sunday Adetoye da Sufeta Ogunleye Stephen da ake aiki a hedkwatar rundunar shirya ta 2, Onika, jihar Legas.
Rundunar ta ce ta kori 'yan sandan saboda kama su da laifin abin da suka kira da fashi da makami, rashawa da aikin assha.
Mataimakin sufeta janar na 'yan sanda, da ke kula da shiyya ta 2, AIG Mohammed Ali ne ya ba da umarnin sallamar jami'an.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ASP Ajaiyi Victor, ogan 'yan fashin ya tsere
Rahotan Daily Trust ya nuna cewa a cafke jami'an 'yan sandan tare da wasu mutum uku kan zargin fashi da makami a jihohin Legas da Ogun.
An ruwaito 'yan sandan tare da tawagar su sun dira wani gida a Obada-Oko a jihar Ogun inda suka yi wa mutanen gidan fashi.
Wani mataimakin sufuritandan 'yan sanda (ASP), Ajaiyi Victor, wanda ya jagoranci fashin, ya tsere, ba a kama shi ba.
Sauran mutum uku da aka kama kamar yadda Vanguard ta ruwaito 'yan kungiyar bijilante ne, sun aikata fashin ranar 23 ga watan Nuwamba 2023.
Yadda aka kama masu laifin
Ko da ta ke bayyana yadda aka kama su, kakakin rundunar na shiyya ta 2, SP Umma Ayuba ta ce:
"Yan sanda suka kafa shingen bincike a hanyoyi bayan kai rahoton fashin, inda aka kama masu laifin amma ASP Ajaiyi Victor ya tsere.
"AIG ya ba da umurnin a sallami jami'an daga aiki, kuma a gurfanar da su gaban kotu tare da 'yan bijilante da aka kama su tare."
A cafke 'yan Arewa da ke kokarin shiga aikin soja karkashin jihar Legas
A wani labarin, rundunar soji ta ce ta cafke wasu matasa shida da suka fito daga jihar Kaduna, a wajen daukar aikin soja.
Wali bidiyo da ya yadu ya nuna yadda matasan suka buga takardun shaidar zama 'yan jihar Legas na bogi, don a dauke su aikin.
Asali: Legit.ng