Emefiele: Dangote Ya Shiga Matsala Bayan EFCC Ta Dira a Babban Ofishinsa, Bayanai Sun Fito
- Da alamu Aliko Dangote ya shiga matsala bayan jami'an Hukumar EFCC ta dira a babban ofishin kamfanin da ke Legas
- Da yammacin yau ne Alhamis 4 ga watan Janairu jami'an EFCC suka fara binciken wasu takardu kan canjin kudade
- Sai dai Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya ki cewa komai komai bayan tuntubarshi da 'yan jarida suka yi kan lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Jami'an Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) sun durfafi babban ofishin kamfanin Dangote da ke jihar Legas.
Jami'an sun dira a ofishin ne don binciken badakalar kudaden canji da ake zargin sun yi da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a kamfanin, cewar The Nation.
Wane mataki EFCC ta dauka kan Dangote?
Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya ki cewa komai komai bayan tuntubarsa da 'yan jarida suka yi kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TheCable ta tattaro cewa wani daga cikin ma'aikatan kamfanin ya tabbatar mata cewa jami'an suna cikin ofishin.
Ma'aikacin ya ce:
"Sun tambayi takardun canjin kudade da aka yi da Emefiele ofishin."
Wasu zarge-zarge ne kan Emefiele bayan dakatar da shi?
Ana zargin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele da badakalar makudan kudade lokacin da ya ke kan kujerar gwamnan babban bankin kasar.
Shugaba Tinubu ya dakatar da Emefiele ne a ranar 9 ga watan Yuni kan zarge-zarge da ake yi a kansa da umartar ci gaba da bincike.
Daga bisani ya umarci fara bincike kan tsohon gwamnan inda daga bisani ya nada Yemi Cardoso a matsayin gwamnan bankin.
Sadiya Farouk ta bayyana dalilin kin amsa gayyatar EFCC
A wani labarin, tsohuwar Ministar jin kai da walwalar jama'a, Sadiya Umar Farouk ta bayyana dalilin kin amsa gayyatar hukumar EFCC kan badakalar kudade.
Hukumar na zargin Ministar Buhari ne da karkatar da naira biliyan 37 na ma'aikatarta yayin da ta ke Minista.
Tun farko hukumar ta gayyace ta a jiya Laraba 3 ga watan Janairu inda ta ki amsa gayyatar amma daga bisani ta ba da dalilai.
Asali: Legit.ng