Gwamnan PDP Ya Ware N11bn a Kasafin Kudin 2024 Domin Cin Abinci da Shakatawa? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnan PDP Ya Ware N11bn a Kasafin Kudin 2024 Domin Cin Abinci da Shakatawa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin jihar Osun ta musanta labarin cewa ta ware N11bn cikin kasafin kuɗin shekarar 2024 domin cin abinci da shaƙatawa a ofishin gwamnan jihar
  • Kwamishinan kasafin kuɗin jihar wanda ya musanta hakan ya bayyana cewa N600m ne kawai aka ware domin hakan
  • Farfesa Ademola Adeleke ya yi bayanin cewa kuɗaɗen sun ƙunshi ofishin gwamna, mataimakinsa da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ta ware N702m domin cin abinci da shaƙatawa ga ofishin gwamna da sakataren gwamnatin jihar a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024 na jihar.

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinan kasafin kuɗi, Farfesa Moruf Adeleke, wanda ya tabbatar da hakan a lokacin da yake nazarin kasafin kuɗin a Osogbo ya ƙaryata labarin da aka yi cewa an ware N11bn domin abinci da nishaɗi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kori SSG Abdullahi Baffa Bichi? Gaskiya ta bayyana

Adeleke ya ce an ware kimanin N8bn domin gudanar da ayyukan ofishin gwamnan jihar.

Gwamna Adeleke ya ware kudin cin abinci da shakatawa
An ware kudin cin abinci da shakatawa ga Gwamna Adeleke Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kuɗaɗen sun haɗa da na ofishin gwamnan, mataimakin gwamnan, shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da sauran hukumomin da ke a ƙarƙashin gudanarwar ofishin gwamnan.

Nawa aka ware domin cin abinci a ofishin gwamnan?

Ya ce N600m ne kacal daga cikin N8bn aka ware domin abinci da nishaɗi, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Ya ce an ware kimanin N3bn ga ofishin sakataren gwamnatin jihar, wanda daga ciki aka ware N102m domin abinci da nishaɗi.

Kwamishinan ya ce an samu cigaba a kuɗin da ake warewa domin gudanar da ayyukan yau da kullum daga 68:32 a shekarar 2023 zuwa 60:40 a shekarar 2024.

Gwamna Adeleke ya naɗa sarakuna

Gwamnatin jihar Osun ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke, ta amince dan naɗin sabbin Sarakuna shida domin cike gurbin masarautu a yankunansu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar NSIPA bayan dakatar da Halima Shehu

An amince da naɗin sabbin Sarakunan ne da ƙarin girma ga wasu Sarakuna 11 a wani zaman majalisar zartaswa na jihar.

Adeleke Na Son Zama Shugaban Ƙasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana aniyarsa ta ƙwadayin neman shugabancin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa yana da tabbacin ya cancanci ya hau kan kujerar shugabancin ƙasar nan, sannan da zarar ya samu dama ba zai bari ta wuce ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng