An Manta da Tudun Biri Bayan Rundunar Sojin Sama Ta Dauki Matakin Tallafawa Jami'anta Kan Hadura
- Yayin da ake ci gaba da jimamin harin bam a Kaduna, hukumar sojin sama ta dauki matakin kare hakan a gaba
- Hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar ya amince da ba da inshora ga dukkan jami'an sojin sama yayin da suke aiki
- Daraktan yada labaran rundunar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet shi ya bayyana haka a yau Laraba 3 ga watan Janairu a Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babban Hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar ya amince da inshora don sojojin sama kasar.
Hassan ya amince da bukatar ce don tallafawa sojin sama da ke cin karo da hatsarin jirgin sama a kasar, Vanguard ta tattaro.
Mene dalilin daukar matakin?
Wannan mataki na zuwa ne bayan sojoji sun jefo bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin ya hallaka mutane fiye da 150 da raunata wasu dama wanda hakan ya da hankulan mutane a kasar baki daya.
Wannan mataki zai shafi dukkan sojojin sama da ke kasar idan wani iftila'in hatsari ya faru da su.
Daraktan yada labaran rundunar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet shi ya bayyana haka a yau Laraba 3 ga watan Janairu a Abuja.
Gabkwet ya ce matakin zai shafi dukkan iyalan sojin da suka mutu sai dai banda bangaren magani da hatsarin ya jawo.
Ya ce wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren babban hafsan sojin wurin tabbatar da samun runduna mai inganci, cewar Daily Post.
Su waye shirin zai shafa?
Sanarwar ta ce:
"Duk da wannan inshora zai shafi dukkan sojin saman Najeriya amma banda sauran matsaloli da hakan ya biyo da su yayin aiki.
"Tabbatar da rundunar mai inganci ya zama dole wurin dakile yawan hatsura da ake samu yayin gudanar da aiki."
Gabkwet ya ce shirin zai shafi ba da diyya ga jami'an da suka mutu da raunuka da kuma biyan kudaden magani.
Izala ta yi Allah wadai da harin Kaduna
A wani labarin, shugaban kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi Allah wadai da harin bam kan masu Maulidi a Kaduna.
Jingir ya ce ba za su yarda da irin wannan lamari ba inda ya bukaci a yi bincike tare da hukunta masu laifi.
Asali: Legit.ng