2024: Tinubu Ya Fadi Biliyoyin Naira da Zai Kashe Wajen Dawo da Shirin Ciyar da Dalibai Abinci

2024: Tinubu Ya Fadi Biliyoyin Naira da Zai Kashe Wajen Dawo da Shirin Ciyar da Dalibai Abinci

  • Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta ware naira biliyan 100 domin dawo da shirin ciyar da dalibai abinci a fadin kasar
  • Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudi na shekarar 2024 da ya zama doka a Abuja
  • Shirin ciyar da dalibai abinci a cewar shugaban kasar zai zama wani abin karfafa guiwar yara don zuwamakarantu, da bunkasa harkar koyarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2024 ya hada da ware naira biliyan 100 domin shirin ciyar da dalibai abinci.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudi na shekarar 2024 da ya zama doka a fadar gwamnati da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin kudin 2024 a Aso Villa, bayanai sun fito

Shirin ciyar da dalibai abinci zai lakume N100bn a gwamnatin Tinubu
2024: Gwamnatin Tinubu za ta kashe naira biliyan 100 akan shirin ciyar da dalibai abinci. Hoto: @officialABAT, @NHGSFP
Asali: Twitter

Leadership ta ruwaito shugaban yana mai cewa shirin zai zama wani abin karfafa guiwar yara don zuwamakarantu da kuma rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar dawo da shirin ciyar da dalibai abinci

Tinubu ya ce:

"Daya daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin kudirin dokar da aka amince da su kwanan nan shi ne ware naira biliyan 100 don ciyar da yara ‘yan makaranta abinci."
"Na yi imanin wannan zai zama abin karfafa guiwar yara wajen shiga makarantu da kuma taimakawa wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin dalibai."

A farkon Disamba 2023, Tinubu ya ba da umarnin sake dawo da shirin ciyar da dalibai abinci tare da ba da umarnin sauya shi daga ma’aikatar jin kai zuwa ma’aikatar ilimi, rahoton Daily Trust.

Shirin wanda aka qaddamar da shi daga baya kuma aka dakatar da shi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai samar da abinci mai gina jiki ga dalibai, har ma da inganta harkar koyo.

Kara karanta wannan

2024: Shugaba Tinubu ya bayyana babban buri ɗaya tal da ya sa ya nemi hawa mulki sau 3 a Najeriya

Tinubu ya dawo da shirin ciyar da dalibai abinci a kananun makarantu

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya sanar da dawo da shirin ciyar da dalibai abinci don rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Gwamnatin da ta shude ta Buhari ce ta kawo shirin don bunkasa harkar koyo da koyarwa, amma daga bisani ta dakatar da shi.

Sai dai gwamnatin Tinubu ta cire shirin daga ma'aikatar jin kai (kamar yadda ya ke a baya) zuwa ma'aikatar ilimi don ganin ya samu muhimmiyar kulawar da ya ke bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.