“Lallai Bai da Kunya”: An Fallasa Wani Dattijo Bayan Ya Aikewa Budurwa Sakonnnin da Basu Dace Ba

“Lallai Bai da Kunya”: An Fallasa Wani Dattijo Bayan Ya Aikewa Budurwa Sakonnnin da Basu Dace Ba

  • Wata matashiya yar Najeriya ta caccaki wani dattijo da ya aike mata da sakonnin da basu dace ba a dandalin X
  • Duk da ta fito karara ta nuna masa bata yi tare da gargadinsa, mutumin ya ci gaba da aike mata da sakonni wanda sam basu yi mata ba
  • Cike da gajiya da halinsa, ta fito bainar jama'a don caccakarsa, lamarin da yasa mutane Allah wadai da shi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya a dandalin X ta nuna gajiyawarta a kan abubuwan da wani dattijo ke yawan yi mata.

Matashiyar mai suna @DeejustDee ta dauki hotunan sakonnin da yake ta aika mata, tare da baje kolin maganganunsa da kuma kin mutunta iyakokinta.

Kara karanta wannan

"Kina son dana?" Wata uwa ta tunkari kyakkyawar budurwa da ta gani a wajen biki a madadin danta

Dattijon ya aike mata da sakon da zai kamata ba
An yi amfani da hotunan don misali ne basu da alaka da labarin Hoto: Jasmin Merdan, Yagazie Emezi/ Getty Images, @deejustdee/X.
Asali: Twitter

An fallasa cin zarafin da wani dattijo ke yi wa budurwa

Duk da ta fito karara ta nuna masa bata ra'ayinsa, mutumin ya ci gaba da aike mata da sakonnin da basu kamata ba har a safiyar sabuwar shekara, ba tare da la'akari da rashin amincewar ta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yana aike mata da sakonni kamar:

"Ina jin cin ki. Ina nufin ina ji dama ace ina tare da ke, kin yi kalar dadi. Kina da lambar wayata? Toh hakan ya yi."

Cike da gajiya da halin mutumin, matashiyar ta yanke shawarar daukar mataki a hannunta.

Ta fito ta fallasa sakonnin mutumin da basu dace ba a shafinta na X, tare da wasu zazzafan kalamai na Allah wadai da ayyukansa.

Ta rubuta:

"Fuskar wani wawan tsoho a safiyar 2024, wannan ba shine karo na farko da yake yin wannan shirmen a akwatin sakona ba kuma ina ta kyale shi yana cin bulus, yanzu ka sake yi sannan na toshe shi. Wwan tsoho, mummunan agwagwa."

Kara karanta wannan

"Ya hadu": Wani mai zanen gida ya kafa tarihi, ya gina zagayayyen gida a kauyensa

Jama'a sun yi martani

Nan take wallafar tata ta ja hankalin jama'a inda suka mara mata baya tare da yin Allah wadai da rashin ta idon mutumin.

@Viktordrai ta yi martani:

"Mijin wata mutane na auren shirme."

@Its_Imperial_ ta yi martani:

"Wannan sabuwar shekarar bata yarje ma kowa ba."

@zealprecious1 ta ce:

"Yi ta jansa. Ci gaba da caccakarsa. Shaidani kuma mugun mutum."

Ga wallafar a kasa:

Mata ta gano sako a wayar miji

A wani labari na daban, wata yar Najeriya ta duba wayar mijinta sannan ta karaya da sakon da ya aikewa daya daga cikin abokan aikinsa a WhatsApp.

Matar auren da ba a bayyana sunanta ba ta yada sakon a dandalin Facebook, yayin da take neman shawara kan abun yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng