Murna Yayin da Tinubu Ya Yi Shirgegen Alkwari da Zai Juya Akalar Kasar a 2024, Ya Fadi Dalili
- Shekarar 2024 za ta zo da abubuwan alkairi bayan Shugaba Tinubu ya yi alkawarin samar da wutar lantarki mai inganci
- Shugaban ya ce ya shiga yarjejeniya da hukumar samar da wutar ta Siemens da ke jamus don inganta wutar a Najeriya.
- Tinubu ya bayyana haka ne a yau Litinin 1 ga watan Janairu yayin jawabin sabuwar shekara a Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tnubu ya yi alkawarin sauya akalar kasar wurin samar da ingantacciyar wutar lantarki.
Tinubu ya ce ya shiga yarjejeniya da hukumar samar da wutar ta Siemens da ke jamus don inganta wutar a Najeriya.
Wane alkawari Tinubu ya yi?
Shugaba ya bayyana haka ne a yau Litinin 1 ga watan Janairu yayin jawabin sabuwar shekara a Abuja, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce shugaban gwamnatin Jamus ya amince da bukatar tasu don inganta wutar a Najeriya don bunkasa kasuwanci.
Ya ce:
“A watan Disamba din nan da ta wuce yayin taron COP28 a Dubai, shugaban gwamnatin Jamus ya amince da bukatar yarjejeniyar don samar da wutar a Najeriya.
“Wannan hobbasa na kamfanin Siemens zai inganta wutar lantarki a Najeriya don kasuwanci da kuma gidaje daidaiku.
“Gwamnatina ta himmatu wurin tabbatar da wutar wanda idan ana son bunkasar komai sai da wutar lantarki a kasa.”
Yaushe aka sanya hannu a yarjejniyar?
Gwamnatin Najeriya da kasar Jamus a watan Disambar 2023 sun rattaba hannu kan yarjejeniya da Siemens da za ta samar da wutar, cewar Daily Post.
Sa hannun an yi shi ne a wani babban taro a kasar Dubai inda Tinubu da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz suka amince da shi.
Buhari ya ji dadin cire tallafin mai
A wani labarin, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa bayan Shugaba Tinubu ya cire tallafin mai a watan Mayu.
Buhari ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba a birnin Katsina yayin wani taro kan matasa.
Tsohon shugaban ya ce ya ji dadi saboda ya yi tsammanin hakan zai rage yawan masu zuwa Daura don kai masa ziyara.
Asali: Legit.ng