Shari’ar Kano: Mata Sun Yi Gangami Don Nuna Goyon Baya Ga Abba Gida-Gida Gabanin Hukuncin Kotun Koli

Shari’ar Kano: Mata Sun Yi Gangami Don Nuna Goyon Baya Ga Abba Gida-Gida Gabanin Hukuncin Kotun Koli

  • Dubunnan mata ne suka yi gangamin nuna goyon baya ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tare da yin addu'o'in samun nasara a Kotun Koli
  • Shugabar taron Hajiya Salamatu Suleiman, ta ce suna da yakinin Allah zai saka tausayi a zukatan alkalan Kotun Kolin su yi wa Abba adalci
  • A cewar Suleiman, Kotun Kolin ce kawai madogarar talaka a fannin shari'a, kuma suna fatan za ta ayyana Abba Kabir matsayin mai nasara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Dubban mata daga Kano ne suka hallara a sha tale-talen 'Silver Jubilee' a wani gagarumin taron nuna goyon baya da addu’o'i gabanin hukuncin da kotun koli za ta yanke kan zaben gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Abba ko Gawuna? An hango wanda zai yi nasara a kotun koli duba da wasu dalilaia

Tare da hada kai don neman yardar Allah, sun gudanar da taron nasu domin rokon ubangiji ya ba Gwamna Abba Yusuf nasara a Kotun Koli.

Mata sun yi taron nuna goyon bayan Abba Gida-Gida a Kano
Dubunnan mata sun yi gangamin nuna goyon baya ga Abba Kabir Yusuf tare da yin addu'o'in samun nasara a Kotun Koli. Hoto: @channelstv
Asali: UGC

Manufar yin gangamin matan a Kano

Yayin da ake jiran hukuncin kotun kolin, matan sun roki alkalan su tabbatar da yin adalci a cikin karar zaben, suna bayyana imaninsu ga hukuncin kotun koli, Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin shugabar gangamin, Hajiya Salamatu Suleiman:

“Muna rokon Allah ya bamu nasara, mun san cewa Kotun Koli ita ce kawai madogarar talaka a shari'ar Najeriya, muna da yakinin alkalan za su yi adalci."

Matan sun jinjinawa kokarin Abba a 2023

Da take bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a mulkinsa na kasa da shekara daya, Salamatu ta ce:

“Ya biya bashin ma’aikatan da suka yi ritaya, ya aurar da ‘ya’yanmu mata, da tabbatar da biyan albashi a kan kari, ya ba masu nakasa karfin gwiwa, sannan ya dauki nauyin ‘ya’yanmu don ci gaba da karatu a jami’o’in duniya."

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: An yi zanga-zanga a Kano kan takaddamar zaben gwamna

Sai dai kuma baya ga taron addu'o'i don samun nasara a kotun, babban burin gangamin shine samar da zaman lafiya a jihar.

Salamatu ta nuna damuwarta kan yadda tashe-tashen hankula ke kara yawaita, da kuma kara dagulewar yanayin siyasa, inda ta jaddada bukatar addu’o’in samun zaman lafiya a Kano.

Hukumar kashe gobara ta sanar da fara daukar sabbin ma'aikata a 2024

A wani labarin, hukumar kashe gobara ta tarayya, ta fitar da sanarwar fara daukar sabbin ma'aikata, daga matakin sakandire zuwa masu takardun digiri.

Legit Hausa ta yi bayani dalla-dalla kan yadda matasa za su nemi aiki a hukumar, duba wannan shafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.