Sabuwar Shekara: Manyan Alkawurra 5 da Tinubu Ya Daukar Wa ’Yan Najeriya a 2024

Sabuwar Shekara: Manyan Alkawurra 5 da Tinubu Ya Daukar Wa ’Yan Najeriya a 2024

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki wasu alkawurra guda biyar da ya ke fatan gwamnatinsa za ta aiwatar a shekarar 2024
  • A ranar Litinin, 1 ga watan Janairu 2024 ne Tinubu ya yi jawabin kai tsaye ga 'yan Najeriya, inda ya zayyana manufofin gwamnatinsa
  • Daga cikin alkawurran, shugaban kasar ya ce zai mayar da tabbatar da abinci ya wadata, wutar lantarki da man fetur sun wadata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - A jawabin kai tsaye da ya gudanar a ranar Litinin, Shugaba Bola Tinubu ya taya 'yan Najeriya murnar shigowa sabuwar shekarar 2024.

Shugaban kasar a jawabinsa ya bayyana manufofin gwamnatinsa da abin da zai mayar da hankali kansu a 2024.

Kara karanta wannan

2024: Abubuwa 10 da Tinubu ya fadawa Najeriya a jawabin shiga sabuwar shekara

Alkawurran da Tinubu ya daukarwa 'yan Najeriya a 2024
Shugaba Tinubu a jawabinsa ya bayyana manufofin gwamnatinsa da abin da zai mayar da hankali kansu a 2024. Hoto: @NGRPresident
Asali: Facebook

Tinubu ya tariyo yadda ya sha fama a hanyarsa ta zama lamba daya a Najeriya tare da jinjinawa kasar kan shafe shekaru 24 a dimokuradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan hawa mulki, shugaban ya kuma dauki wasu alkawurra guda biyar, Vanguard ta ruwaito.

Ga jerin alkawurran da Shugaba Tinubu ya dauka:

1. Samar da wadatacciyar wutar lantarki

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala dasa layuka da cibiyoyin samar da wutar lantarki a fadin kasar a shekarar 2024.

Ya ce:

"Gwamnatina na sanar da muhimmancin wutar lantarki, shi ya sa a taron dumamar yanayi a Dubai, na shawo kan shugaban Jamus Olaf Scholz, ya amince zamu kaddamar da shirin makamashi na Siemen a Najeriya."

2. Dawo da tace man fetur a Najeriya

Da ya ke jawabi kan tace man fetur a Najeriya, Bola Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Zai Fito Ya Yiwa ’Yan Najeriya Don Sanin Abin da Zai Biyo Baya a 2024

"A shekarar 2024, za mu tabbatar mun farfado da matatun man fetur da suka hada da matatar mai ta Fatakwal, sannan matatar mai ta Dangote za ta taimaka wajen cimma hakan."

3. Bunkasa samar da abinci

A shekarar 2024, Tinubu ya sha alwashin kara kaimi wajen noma hekta 500,000 ta shinkafa, masara, dawo da sauransu a fadin Najeriya don samar da wadataccen abinci kuma mai sauki.

A cewarsa:

"Domin tabbatar da abinci ya wadata kuma a farashi mai sauki, za mu kara kaimi wajen noman rani da damina, mun fara da Jigawa, inda muka noma hekta 120,000 a Nuwamba, 2023."

4. Bunkasa saka hannun jari a cikin gida da waje

Domin bunkasa saka hannun jari a ciki da wajen Najeriya a 2024, Tinubu ya sha alwashin samar da saukakakkiyar hanya ga 'yan kasuwa.

Ya ce:

"A wannan shekarar, za mu hanzarta wajen daidaita haraji da saukaka kasuwanci, hakan zai bamu damar shigo da masu saka jari daga waje, da bunkasa saka jarin a cikin gida."

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Malamin addini ya yi hasashe kan 2024, ya jero masifu 4 a mulkin Tinubu

5. Mayar da hankali kan: Tsaro, amar da aiki, kawar da fatara, da sauran su

A jawabin Shugaba Tinubu kasafin kudin 2024:

"A kasafin 2024 da na gabatarwa majalisar tarayya, gwamnati na ta mayar da hankali kan tsaron kasa, samar da aiki, daidaita tattalin arziki, bunkasa saka hannun jari,
"Haka zalika na karkata kan kawar da fatara, gina al'umma da sauran su saboda hakan ne kawai zai cimma burina na ganin Najeriya ta samu ci gaba a 2024."

"Zo ka nema": Hukumar kashe gobara ta sanar da fara daukar sabbin ma'aikata

Hukumar kashe gobara ta tarayya na ta sanar da fara daukar kwarararru da masu karatun sakandire aiki, ta na neman matasa 'yan Najeriya su jaraba sa a.

Ranar Laraba 27 ga watan Disamba aka bude shafin cike bukatar neman aikin, kuma Legit Hausa ta yi bayanin yadda za a nemi aikin a nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.