Yan Sanda Sun Ceto Gomman Mutanen da Yan Bindiga Suka Sace Bayan Kazamin Artabu
- Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta tabbatar da ceto wasu mutum 24 da ƴan bindiga suka y garkuwa da su
- Rundunar ƴan sandan ta ceto mutanen ne waɗanda aka sace a yankin Adogo da ke ƙaramar hukumar Ajaokuta ta jihar
- Kwanishinan ƴan sandan jihar ya yaba wa jami'an ƴan sandan bisa wannan nasarar da suka samu tare buƙatar al'ummar jihar da su cigaba da ba su haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Kogi tare da haɗin gwiwar sojoji da ƴan banga sun ceto mutum 24 da wasu masu garkuwa da mutane suka sace a jihar.
Masu garkuwa da mutanen dai sun sace mutanen ne a yankin Adogo da ke ƙaramar hukumar Ajaokuta a jihar, cewar rahoton Daily Trust.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, SP William Aya, ne ya bayyana haka a daren jiya Asabar, inda ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ƴan sandan ta ce waɗanda aka ceton sun haɗa da ɗalibai 11 da malamai uku, inda ta jaddada cewa ana cigaba da kokarin cafke ƴan bindigan da suka tsere, rahoton PM News ya tabbatar.
Yadda ƴan sanda suka ceto mutanen
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"A ranar Asabar 30 ga watan Disamba, kwamishinan ƴan sandan jihar Kogi, CP Bethrand C. Onuoha, ya tura ƙarin tawaga ta musamman wacce ta ƙunshi sashin gaggawa zuwa yankin domin shiga cikin tawagar dake ƙarƙashin jagorancin DPO, SP Sule Musa."
"Yayin da tawagar ke kutsawa cikin daji, ƴan bindigan sun hango su daga maboyarsu, sannan suka buɗe wa tawagar wuta."
"A yayin musanyar wutar da aka yi, bisa ga ƙarfin makaman tawagar, an tilasta ƴan bindigan arcewa tare da barin mutanen da suka sace."
CP Onuoha, wanda ya yaba da ƙoƙarin jami'an, ya bukaci al'ummar jihar da su kasance masu bin doka da oda, sannan su cigaba da haɗa kai da ƴan sanda da sauran jami’an tsaro ta hanyar ba da bayanai masu inganci a kan lokaci da kuma sahihan bayanai kan ayyukan masu aikata laifuka a jihar.
Ƴan Sanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan sanda sun samu nasarar daƙiƙe yunƙurin yin garkuwa da wasu ma'aurata da ƴan bindiga suka yi a Kaduna.
Tawagar ƴan sandan ta kuma fatattaki ƴan bindigan da suka kawo farmakin tare da ceto ma'auratan da aka yi yunƙurin sacewa.
Asali: Legit.ng