Ba a Gama Jimamin Mutuwar Mutum 190 Ba, Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Plateau
- Ana tsaka da jimamin mutanen da aka halaka a jihar Plateau, ƴan bindiga sun sake kai wani sabon hari a jihar
- Miyagun ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Durbi cikin ƙaramar hukumar Jos ta Gabas inda suka halaka wani uba da ɗansa
- Ƴan banga da mutanen ƙauyen sun yi fito na fito da ƴan bindigan inda suka daƙile harin tare da kashe ɗaya daga cikin maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun halaka mutum biyu a wani hari da suka kai a ƙauyen Durbi da ke gundumar Shere a ƙaramar hukumar Jos ta Gabas a jihar Plateau.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa harin ya faru ne da daren Asabar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutanen ƙauyen biyu, uba da ɗansa.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da jihar bata gama murmurewa daga mutuwar sama da mutum 190 ba a harin jajibirin Kirsimeti da aka kai a ƙananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin riƙon ƙwarya Markus Nyam ya tabbatar da kai harin a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyen ne cikin dare da halaka wani uba da ɗansa, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Ƴan banga sun fatattaki ƴan bindigan
Nyam ya kuma bayyana cewa ƴan banga da mutanen ƙauyen sun yi artabu da maharan wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaya daga cikin maharan yayin da wasu suka gudu.
Wata majiya ta ce mutanen ƙauyen na tsare da gawarwakin, ciki har da ta ɗaya daga cikim maharan da aka halaka.
Ɗaukin gaggawa da rundunar haɗin gwiwa ta jami'an tsaron 'Operation Safe Haven' ya sanya maharan ba su tafka ɓarna sosai ba.
IGP Ya Gana da Gwamna Mutfwang
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban Sufeta Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya kai ziyara jihar Plateau kan harin da ƴan bindiga suka kai a jihar.
IGP a yayin ziyarar ya gana da gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, inda ya bayar da umarnin tura tawagar tsaro ta musamman zuwa jihar.
Asali: Legit.ng