Kasafin 2024: Ana Rashin Kudi, ‘Yan Majalisa Sun Kara Naira Biliyan 147 a Kasonsu

Kasafin 2024: Ana Rashin Kudi, ‘Yan Majalisa Sun Kara Naira Biliyan 147 a Kasonsu

  • ‘Yan majalisar tarayya sun kara kasafin kudinsu na 2024 a kan lissafin da Bola Ahmed Tinubu ya yi
  • Duk da kalubalen da Najeriya ta ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki, kudin kashewar ‘yan siyasan ya karu
  • A maimakon su kashe kusan N200bn, Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai sun warewa kan su N344bn

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A rahoton Premium Times aka fahimci ‘yan majalisar tarayya sun yi wa kan su karin makudan kudi kan abin da za su kashe.

A maimakon N27.5tr da Bola Ahmed Tinubu ya gabatar, Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai sun maida kasafin 2024 ya zama N28.7tr.

Kasafin kudin Tinubu
Majalisa ta kara kasafin kudin 2024 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kasafin kudin 2024 ya karu

An samu karin N1.2tr ne a daidai lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ta ke rokon mutane su yi hakuri da zafin tsare-tsaren tattalinta.

Kara karanta wannan

Majalisar UN tayi maganar rayuka 190 da aka kashe a Najeriya, Tinubu yana hutu a Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce halin da aka shiga bai hana majalisar tarayya kara kudin da za ta kashe ba bayan ta gama aiki na tsawon makonni.

Kasafin 'yan majalisa a tarihi

Tun daga kasafin kudin shekarar 2011 har zuwa 2014, abin da ‘yan majalisar tarayya su ka kashe bai taba bambanta daga N150bn ba.

A 2015 aka rage kasafin zuwa N130bn a sakamakon karyewar farashin mai a duniya.

Sannu a hankali aka rage kasafin majalisar zuwa N125bn da N128bn lokacin da Muhammadu Buhari yake mulki a 2021 da 2022.

A shekarar karshe ta Buhari, an warewa ‘yan majalisar tarayya har N228bn.

2024: 'Yan majalisa sun yi karin N147bn

Da aka kawo kundin kasafin shekarar nan, ‘yan majalisar sun kara kudinsu daga N169bn zuwa N228bn kamar yadda aka yi yanzu.

Mai girma Bola Tinubu a kasafin da ya gabatar, ya zaftare adadin da kusan N30bn, ya rage wannan kudi a lissafin 2024 zuwa N197bn.

Kara karanta wannan

Abdussamad Rabiu ya hadu da Tinubu, ya fadi abin da zai faru da farashin simintin BUA

Da ‘yan majalisa su ka gama aikinsu sai ga shi an kara N147bn a kan kudin zuwa N344bn, ba a taba ganin irin wannan a tarihi ba.

Aiki a kan kasafin kudin 2024

Kafin nan an samu labari cewa Majalisar dattawa za ta yi zama kan kasafin kuɗin shekarar 2024 da Bola Tinubu ya gabatar masu.

An ji Sanatocin kasar za su haɗu domin amincewa da kasafin kuɗin da za a kashe a shekara mai zuwa wanda ya kai kusan N30tr.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng