An Nada Tinubu da Shettima Sarautun Gargajiya a Abia, Bayanai Sun Fito
- Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun samu karramawar sarautar gargajiya a jihar Abia
- An karrama shugaban da mukamin Omezeri Igbo I daga manyan masu sarautar gargajiya a jihar
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ya wakilci shugaban wanda shi ma aka karrama shi da Enyioma Ndigbo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia - Masu sarautar gargajiya a jihar Abia sun karrama Shugaba Tinubu da matsayin Omezeri Igbo I a jihar.
Tinubu ya samu karramawar ce a yau Juma'a 29 ga watan Disamba, kamar yadda The Nation ta tattaro.
Wane sarauta Tinubu da Kashim suka samu a Abia?
Bikin ya faru ne yayin kaddamar da wani aiki da tarbar mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shi ya wakilci shugaban wanda shi ma aka karrama shi da Enyioma Ndigbo.
Har ila yau, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya samu karramawar Dike Ndemamba.
Wace sarauta kakakin Majalisa ya samu?
Yayin da kakakin Majalisar Wakilai, Tajudden Abbas ya samu mukamin Onunekuroha, cewar Concise.
Wannan na zuwa ne yayin da Shugaba Tinubu ya tafi jihar Legas don hutun bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.
A ranar Alhamis ce 21 ga watan Disamba Tinubu ya tafi jihar yayin da Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun bukukuwan.
Har ila yau, ziyarar hutun shugaban ya bar baya da kura bayan ya halarci sallar Juma'a da Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Mutane da dama a Najeriya sun yi ta cece-kuce kan lamarin inda aka gano gwamnan ya na ta girgiza kai alamun ya na fahimtar abin ake fada.
Aiyedatiwa ya fadi abin da Tinubu ya ce masa a Legas
A wani labarin, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya bayyana ainihin abin da Shugaba Tinubu ya fada yayin da ya kai ziyara a Legas.
A jiya Alhamis 28 ga watan Disamba ce Aiyedatiwa ya je wurin Tinubu inda ya ce ya shawarce shi da ya rike mutanen jihar.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu ya rasu a ranar Laraba 27 ga watan Disamba a Jamus.
Asali: Legit.ng