Matawalle Ya Fusata Kan Tsaro, Ya Tura Zazzafan Gargadi Ga Sabbin Sojin da Suka Samu Karin Girma

Matawalle Ya Fusata Kan Tsaro, Ya Tura Zazzafan Gargadi Ga Sabbin Sojin da Suka Samu Karin Girma

  • Bello Matawalle, karamin ministan tsaro a Najeriya ya gargadi sojojin da suka samu karin girma kan aiki tukuru
  • Matawalle ya bayyana haka ne jiya Alhamis 28 ga watan Disamba yayin bikin karin girman ga sojojin
  • Hausa Legit ta ji ta bakin wani jami'in tsaro kan wannan matsala ta tsaro da ya addabi kasar baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ta tura gargadi ga sabbin Janar-janar da suka samu karin girma.

Matawalle ya gargadi sojojin ne da su dage wurin tabbatar da kawo karshen rashin tsaro da ya addabi Arewa maso Yamma da kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Yakar yan ta’adda da makaman Yakin Duniya II tsohon yayi ne

Matawalle ya tura gargadi n karshe ga sojin Najeriya kan matsalar tsaro
Matawalle ya gargadi sojoji kan dakile matsalar tsaro. Hoto: Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Wane gargadi Matawalle ya yi ga sojojin?

Yayin kaddamar da su a jiya Alhamis 28 ga watan Disamba, Bello ya ce dole su kara kaimi da kuma neman hadin kai don dakile matsalar tsaron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan karin girma da Burgediya Janar 47 suka samu zuwa mukamin Manjo Janar, cewar TheCable.

Karamin ministan ya ce an kara musu girma ne saboda kwarewa sa kuma aiki tukuru da suke da shi bayan jajircewa a aikin.

Ya ce:

"Wannan sakamako ne na kwarewar aiki da kuka nuna da kuma aiki ba tare da son kai ba."

Wane martani hafsan sojin kasar ya yi?

Daraktan yada labarai na rundunar, Onyema Nwachukwu a cikin wata sanarwa ya ce ministan ya taya wadanda suka samu karin girman a madadin Shugaba Tinubu.

A martaninshi, Hafsan sojin kasar, Taoreed Lagbaja ya ce ya zama dole ko wane daga cikinsu ya zage damtse don ganin an samu abin da ake nema.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

Lagbaja ya kuma tunatar da su cewa wannan karin girma na dauke da babban kalubale a gabansu da ke bukatar sauke wa, cewar PRNigeria News.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani jami'in soja da ya bukaci a boye sunansa kan wannan lamari.

Ya ce matsalar da ake samu shi ne 'yan bindigan suna samun bayanan sirri kamar yadda Sarkin Musulmi ya fada.

Ya ce:

"Dole ne a samu hadin kan jama'a da kuma bayan sirri don kawo karshen matsalar tsaron."

Sultan ya yi magana kan rashin tsaro

A wani labarin, Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar ya bayyana takaici kan yadda rashin tsaro ke kara ta'azzara a Najeriya.

Sultan ya ce matsalar da ake samu ita ce duk wani matakin da soji za su dauka maharan su na sane.

Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa musamman a yankunan karkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.