Bayan Kashe Bayin Allah 175 a Jiha Ɗaya, Miyagu Sun Sake Kai Mummunan Hari, Sun Tafka Ɓarna

Bayan Kashe Bayin Allah 175 a Jiha Ɗaya, Miyagu Sun Sake Kai Mummunan Hari, Sun Tafka Ɓarna

  • Miyagu sun sake kai hari wani kauye a karamar hukumar Bakkos kwanaki ƙalilan bayan kashe rayuka 195 a Filato
  • Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar, Monday Kassah, ne ya tabbatar da harin, ya ce maharan sun kona gidaje amma ba su kashe kowa ba
  • Ya kuma bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu a harin jajibirin kirsimeti tsakanin Asabar da Talata ya kai 195

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Kwanaki ƙalilan da suka shige ne wasu mahara ɗauke da makamai suka farmaki kauyuka da dama a ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Sai dai bayan wannan mummunan hari na daren Asabar da safiyar Talata, wasu tsageru sun kuma kai hari kauyen Budel da ke yankin Tangur a Bukkos jiya Alhamis da daddare.

Kara karanta wannan

Majalisar UN tayi maganar rayuka 190 da aka kashe a Najeriya, Tinubu yana hutu a Legas

An sake kai hari jihar Filato.
Bayan Kisan Mutane Sama da 150, Miyagu Sun Kara Kai Hari Kauyen Jihar Plateau Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Shugaban ƙaramar hukumar Bukkos, Monday Kassah, ya ce maharan sun shiga garin da daddare, suka ƙona tare da lalata gidajen bayin Allah, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Kassah ya yi bayanin cewa babu wanda ya rasa ransa a wannan sabon harin saboda ɗaukin da dakarun tsaro suka kai a kan lokaci.

Adadin mutanen da aka kashe ya kai 195

Yayin da yake bayar da bayani kan harin jajibirin ranar Kirsimeti, kantoman ƙaramar hukumar ya bayyana adadin wadanda suka mutu kawo yanzu da 195.

Ya kuma ƙara da cewa har yanzun ana kan aikin ceto domim zaƙulo sauran mutanen da suka ɓata tun lokacin da aka kai harin.

Daga cikin adadin, an kashe 148 a karamar hukumar Bokkos, 19 a karamar hukumar Mangu, 27 a Barkin Ladi, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jimami yayin da babban mai sarautar gargajiya ya rasu ya na da shekaru 61 a duniya, bayanai sun fito

Asarar da mutane suka yi a hare-haren

An kona gidaje 1,290 a karamar hukumar Bokkos, an kona gida daya a karamar hukumar Mangu, haka kuma na Barkin Ladi har yanzu ba a tantance ba.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi Allah wadai da wannan tashin hankalin, inda ya kira hare-haren da “barna, zalunci da rashin gaskiya”.

"Gwamnati za ta dauki kwararan matakai don dakile hare-haren da ake ci gaba da kaiwa kan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba," in ji Gyang Bere, kakakin gwamnan.

Yan bindiga sun aiko da sako kan ɗalibai mata da suka sace

A wani rahoton kuma ‘Yan bindiga sun yi barazanar kashe wasu daga cikin daliban jami’ar FUG da aka dauke watanni da su ka wuce.

Iyayen daliban jami’ar ta Gusau sun roki gwamnatin Najeriya ta sa baki domin yaransu su dawo gida cikin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262