Yanzu Aka Fara: Miyagu Sun Yi Alkawarin Sake Kai Hari Bayan Kashe Mutum 195 a Filato
- Kungiyar Middle-Belt Forum ta ce ‘yan ta’adda sun rubuto wasika cewa za su kuma kai wani hari a jihar Filato
- Mista Stanley Kavwam ya shaidawa duniya wannan da aka yi hira da shi a matsayinsa na shugaba a MBF
- Ana zargin jami’an tsaron Najeriya da cafke marasa laifi, yayin da mutane su ke cigaba rayuwa cikin barazana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Jos – A daidai lokacin da al’umma ba ta gama makokin dinbin mutanen da aka kashe a Filato ba, an ji ana neman sake kai wani harin.
Kungiyar Middle-Belt Forum (MBF) ta mutanen tsakiyar Najeriya ta ce an rubuta takardar kawo hari, labarin ya zo a jaridar nan ta Vanguard.
‘Yan ta’addan sun aikowa mutanen Pushit a karamar hukumar Mangu wasika cewa za su sake kawo hari kwanaki da kashe mutane har 195.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a kai wani hari a Filato yau?
A yau Juma’a, 29 ga watan Disamba 2023 ne aka yi alkawarin kawo wani harin na dabam. Jaridar Punch ta fitar da wannan labari a dazu.
Mataimakin shugaban kungiyar MBF na kasa, Stanley Kavwam, ya tabbatar da haka da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin Arise a jiya.
Stanley Kavwam ya ce wasu mutane da ba a san su ba sun jefo wasiku a garin Pushit, suna barazanar kawo wani mummunan harin a yau.
"A yayin da na ke tuki daga Jos zuwa nan, an kira ni cewa an aiko takarda zuwa kauyenmu ‘yan ta’adda za su kawo hari a ranar 29 ga Disamba."
- Stanley Kavwam
Kavwam ya yi ikirarin jami’an tsaro su na kama mutanen da ba su da hannu a harin da aka kai, a cewarsa sojoji sun san masu yin aika-aikar.
Kashe-kashen Filato ya jawo Allah-wadai
A daidai lokacin da Kavwam yake wannan bayani, majalisar dinkin duniya ta bukaci ayi bincike na musmaman a kan sabon harin da aka kai.
Wannan shi ne kiran da ‘yan Arewa da ke majalisar wakilan tarayya da marasa rinjaye karkashin jagorancin Hon. Kingsley Chinda suka yi.
An kai hari a Filato, ina shugaban kasa?
An rahoto cewa shugaban kungiyar PFN ta kiristoci, Bishof Francis Oke ya bukaci Bola Ahmed Tinubu ya yi binciken yadda aka rasa rayuka.
Wasu fastoci sun bukaci shugaban kasa ya dakatar da hutun kirismeti da na sabuwar shekara da yake yi a Legas, ya koma ofishinsa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng