Tsohuwar Jakadar Najeriya Ta Shigar da Karar Ministan Buhari a Kotu a Kasar Waje
- Lilian Onoh za tayi wata sabuwar shari’a da Geoffrey Onyeama da Gabriel Aduda a birnin Texas a kasar Amurka
- Tsohuwar Jakadar tana tuhumar abokin fadanta da zarginta da satar kudi, laifin da ta ke ikirarin ba ta aikata ba
- Lauyan Onoh ya hada da gidan jarida a karar, ya ce da su aka yi amfani wajen bata sunanta ta a gaban idon duniya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
United States - Lilian Onoh wanda ta taba zama Jakadar Najeriya zuwa kasar Namibiya ta yi karar Geoffrey Onyeama da Gabriel Aduda.
Rahoton Premium Times ya ce tsohuwar Jakadar ta shigar da karar wadannan mutane ne a wata kotun lardin Arewacin Texas a Amurka.
Geoffrey Onyeama ya bar gwamnati
Geoffrey Onyeama ya yi shekaru bakwai a matsayin Minista na harkokin wajen Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shi kuma Mista Gabriel Aduda ya taba zama Babban sakatare a ma’aikatar waje, yanzu yana rike da mukamin a ma’aikatar mai.
Lauyan da ya shigar da karar a madadin Lilian Onoh a kotun da ke kasar ta Amurka a ranar Juma’a da ta wuce shi ne Steven Thornton.
Mai shari’a Jane J. Boyle zai saurari karar, amma ba a yanke lokacin da za a fara shari’a ba.
Lauyan Onoho sun je kotu
Takardun da jaridar ta ci karo da su, sun tabbatar da tsohuwar jami’ar gwamnatin tana karar har da gidan jaridar Sahara Reporters a kotu.
Lauyar Onoh ta ce an yi amfani da Sahara Reporters da ke Amurka a wajen bata ta.
A birnin tarayyar Najeriya watau Abuja, Onyeama ya kai Onoh kara a kotu, yana zarginta da kalaman da za su iya bata shi wajen jama’a.
Saboda haka Onoh wanda ‘yaruwar tsohon Ministan tarayyar ce ta kai korafi gaban NJC domin hukunta alkalin da ke sauraron shari’arsu.
Onyema ya kai Onoh kotu
Tsohuwar surukin ‘dan siyasar ta zargi Alkalai da rashin adalci, don haka ta ce a hukunta su bayan tayi ta jifan Onyeama da zargin sata.
The Cable ta ce Onoh ta ce rahoton da aka fitar a Sahara Reporters game da tsige ta daga ofis kan zargin satar N500m ba gaskiya ba ne.
Mr Thornton yace har da hoton jami’ar aka nuna a labarin, hakan ya nuna da gan-gan aka yi wannan saboda a bata sunan a idon duniya.
Halin da ake ciki a Najeriya
A Najeriya, jama’a sun shiga matsin lambar tattali a shekarar 2023 saboda tsare-tsaren da gwamnati da bankin CBN su ka fito da su.
Godwin Emefiele ya canza N200, N500 da N1000 kuma ya rage adadin kudin da za a iya cirewa a rana, daga baya aka janye tallaifn mai.
Asali: Legit.ng