Yan Sanda Sun Sheke Miyagun Yan Bindiga 6 a Jihar Bauchi

Yan Sanda Sun Sheke Miyagun Yan Bindiga 6 a Jihar Bauchi

  • Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta sami nasarar halaka wasu miyagun ƴan bindiga mutum shida
  • Jami'an ƴan sandan tare da haɗin gwiwar mafarautan Ahmed Ali Kwara sun halaka ƴan bindigan ne a ƙaramar hukumar Ningi
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da hakan ya kuma bayyana cewa an ƙwato kayayyaki masu yawa a hannun ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi tare da haɗin gwiwar mafarautan Ahmed Ali Kwara sun yi nasarar kashe wasu ƴan bindiga.

Tawagar jami'an tsaron ta halaka ƴan bindigan ne guda shida da ke addabar al'umma a ƙaramar hukumar Ningi ta jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mai garkuwa da mutane da ke sayar da yara

Yan sanda sun halaka yan bindiga a Bauchi
Yan sanda sun yi ajalin yan bindiga a jihar Bauchi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kwamishinan ƴan sandan jihar Auwal Musa Muhammad, ya bayyana hakan a ranar Laraba a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Ningi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sheƙe yan bindigan

Kwamishinan ya ce sun gudanar da aikin mayar da martani ne bisa kisan gilla da aka yi wa mutum takwas da suka haɗa da basaraken Kada da ƙauyen Gamji da ke ƙaramar hukumar a watan Yuli.

Muhammad ya bayyana cewa, biyo bayan kisan gillar da aka yi wa mutum takwas, rundunar ta haɗa wata tawagar jami’an tsaro tare da jami’an tsaro na Ahmed Ali Kwara, rahoton Tribune ya tabbatar.

Shugaban ƴan sandan ya ce rundunar haɗin guiwar ta yi artabu da ƴan bindigan ne a ranar 26 ga watan Disamban 2023, da misalin ƙarfe 4:00 na dare, inda suka kashe shida daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka cafke wata daliba mai ba yan bindiga bayanai, ta tona asiri

An ƙwato kayayyaki masu yawa a hannunsu

Muhammad ya bayyana cewa an kwato bindigogi ƙirar AK47 guda biyu, harsasai guda 55, jigida guda huɗu da babu komai a ciki, da kuɗi naira miliyan 4.5, motar Golf 3 ɗaya, sabbin layukan waya guda bakwai, da wayoyi guda shida daga hannun ƴan bindigan.

Kwamishinan ya ce sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da wayoyin Android 11, ƙananan wayoyi guda huɗu, batirin wayar hannu guda 24, da katunan waya guda 190.

Kwamishinan ya ƙara da cewa:

"Bincike na farko ya nuna cewa ƴan bindigan cikin makonni biyu, sun mamaye ƙauyuka huɗu da ke kusa da Ningi, waɗanda suka haɗa da Bukutumbe, Iyayi, Kayadda da Gamji, inda suka harbe mutum huɗu tare da kashe dan banga ɗaya a Bukutumbe."
"Sun zarce zuwa ƙaramar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa inda suka yi garkuwa da mata biyu na shugaban ƙaramar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa."

Kara karanta wannan

Ana cikin bikin Kirsimeti yan bindiga sun kai mummunan hari a jihar Arewa, sun halaka mutum 6

Ƴan Sanda Sun Cafke Mai Ba Ƴan Bindiga Bayanai

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Neja ta samu nasarar cafke wata ɗaliba mai ba ƴan bindiga bayanai.

Ɗalibar wacce ke karatu a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Neja ta shiga hannu ne bayan an cafke wani ƙasurgumin ɗan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng