Hukumar Kashe Gobara Ta Tarayya Za Ta Fara Daukan Sabbin Ma’iakata, Jerin Abubuwan Da Ake Bukata
- Hukumar kashe gobara ta tarayya ta sanar da fara daukar ma'aikata, an nemi 'yan Najeriya da suka cancanta da su nemi aikin ko za su dace
- An raba daukar aikin a gida biyu, inda hukumar ta ware bangaren kwararru da kuma masu ilimin sakandire kawai
- Ana so wadanda za su nemi aikin su kasance suna da tsayin minita 1.65 ga maza, sai kuma mita 1.60 ga mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Hukumar kashe gobara ta tarayya na neman kwarararru da masu karatun sakandire su cike bukatar neman aiki a hukumar da ta bude kofa.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga shafin hukumomin tsaron farar hula, gidajen gyaran hali, hukumar kashe gobara da shige da fice (CDCFIB) a yanar gizo.
Yadda za a nemi aikin
Ranar Laraba 27 ga watan Disamba aka bude shafin cike bukatar neman aikin, a shiga nan https://cdcfib.career.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dole ne a tura bukatar neman aikin cikin makonni shida da fara daukar aikin.
Guraben aiki
A cewar sanarwar daukar aikin, an bude guraben daukar aikin kamar haka:
Rukunin A: INSPECTORATE CADRE
Sufetan kashe gobara (IF), matakin albashi na CONPASS 07 (ma'aikacin lafiya)
Dole ne mai neman wannan aikin ya zama kwararren ma'aikacin lafiya (RN), kwararren unguwar zoma (RM), kwararren ma'aikacin jinya ko unguwar zoma (RNIM) da ya yi karatu daga manyan makarantu.
Mataimakin Sufetan kashe gobara (AIF), matakin albashi na CONPASS 06
Dole ne mai neman wannan aikin ya zama yana da shaidar kammala karatun NCE ko Diploma ta kasa (ND), a fannin da ya shafi aikin, kuma ya gama a babbar makaranta.
Rukunin B: ASSISTANT CADRE
Mataimakin jami'in kashe gobara na II (FA II), matakin albashi na CONPASS 04
Dole ne mai neman wannan mukamin ya kasance yana da shaidar kammala sakandire, SSCE/NECO, ko wata shaidar ta daban, amma ya samu sakamako mai kyau a darussa biyar.
Mataimakin jami'in kashe gobara na III, ana neman kwararren direba, matakin albashi na CONPASS 03
Dole ne mai neman wannan mukamin ya kasance yana da shaidar kammala sakandire, SSCE/NECO, ko wata shaidar ta daban, amma ya samu sakamako mai kyau a darussa biyar.
Wanda zai nemi wannan aikin kuma mai lasisin tukin motocin da suka fada rukunin (E) zai fi samun fifiko.
Abubuwan da ake bukata don neman aikin
- Dole mai neman aikin ya zama haihuwar Najeriya
- Mai neman aikin ya mallaki shaidar kammala karatu
- Mai neman aikin ya zama mai shekara 18 zuwa 35
- Mai neman aikin ya zama yana da tsawon mita 1.65 (maza) da mita 1.60 (mata)
- Mai neman aikin ya zama yana da fadin kirji da ya haura 0.87 (maza)
- Ilimin kwamfuta na da muhimmanci wajen neman aikin (amma ba dole ba ne)
Gobara ta tashi a gidan tsohon gwamna, mutum biyu sun mutu
A wani labarin, mutum biyu ne suka rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a gidan tsohon gwamnan Oyo, Adebayo Alao-Akala, Legit Hausa ta ruwaito.
Shugaban hukumar kashe gobara na Obomoso, Mr Oluwaseyi Awogbile, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta fara a safiyar Litinin, 18 ga watan Disamba, 2023.
Asali: Legit.ng