Awanni Da Mutuwar Gwamna, Tsohon Shugaban Majalisa, An Rasa Mai Mulki a Najeriya
- Gwamna Nasiru Idris ya sanar da cewa wani shugaban karamar hukuma a jihar Kebbi ya rasu a makon nan
- Hadimin Gwamnan Kebbi, Ahmed Idris ya ya ce yau Alhamis ne Hon. Zayyanu Muhammad Bello ya bar duniya
- Nan gaba za a fadi lokacin jana’izar tsohon shugaban hukumar ta Maiyama yadda addinin musulunci ya tsara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta fitar da sanarwar rasuwar shugaban karamar hukumar Maiyama a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun bakin Mai girma gwamna Nasir Idris, Ahmed Idris ya sanar da mutuwar ga manema labarai dazu.
Punch ta ce Ahmed Idris ya shaidawa ‘yan jarida cewa Alhaji Muhammad Bello ya rasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasuwar Zayyanu Muhammad Bello
Marigayi Muhammad Bello ya yi ban-kwana da duniya ne bayan ya dauki lokaci yana fama da larurar rashin lafiya.
A sanarwar da aka fitar a safiyar ranar Alhamis, an tabbatar da yau za a birne tsohon shugaban karamar hukumar.
Gwamnatin Kebbi ta ce marigayin ya rasu ne a asibitin koyon aiki ne jami’ar Usman Danfodio da ke garin Sokoto.
Ta'aziyyar gwamnatin jihar Kebbi
"Cikin takaici da bakin ciki, muna sanar da mutuwar Hon. Zayyanu Muhammad Bello, shugaban karamar hukumar Maiyama.
Ya rasu ne asibitin koyon aiki jami’ar Usman Danfodio, Sokoto bayan rashin lafiya.”
- Ahmed Idris
Ana sa ran cewa an jima kadan za a sanar da lokacin birne Zayyanu Muhammad Bello kamar yadda addini ya tanada.
Mutuwar masu mulki
Wasu sun ce da kimanin karfe 2:00 na ranar yau ne za a birne marigayin a gidansa da ke garin Maiyama a jihar Kebbi.
A 'yan watannin bayan nan an rasa shugabannin kananan hukumomin Karasuwa, Lokoja da Bebeji a Yobe, Kogi da Kano.
...Gwamna, Na'Abba sun bar duniya
A safiyar Laraba aka ji labari Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba ya rasu a gidansa da ke Abuja, yana ‘dan shekara 65 a duniya.
Tun jiya aka birne Ghali Na’Abba a garin Kano, manyan mutane da-dama sun halarci jana’izar tsohon shugaban majalisar.
A makon nan ne kuma Mai girma Rotimi Akeredolu, danginsa sun ce za a tsaida lokacin da za a birne tsohon gwamnan.
Asali: Legit.ng