Akeredolu: Tinubu Ya Girgiza da Mutuwar Gwamnan Ondo, Ya Tura Sako Ga Gwamna Mai Jiran Gado

Akeredolu: Tinubu Ya Girgiza da Mutuwar Gwamnan Ondo, Ya Tura Sako Ga Gwamna Mai Jiran Gado

  • Shugaba Tinubu ya kadu bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a yau Laraba 26 ga watan Disamba
  • Tinubu ya bayyana Akeredolu a matsayin jajirtacce wanda ya ba da gudunmawa wajen kwato mulki a shari'ar zaben jihohin APC
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin a bangaren yada labarai ta zamani, Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba 27 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Shugaban ya ce marigayin mutum ne wanda ba shi da tsoro inda ya ce an tafka babban rashi, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Mutuwar Akeredolu: Shin Aiyedatiwa ne zai zama sabon gwamnan Ondo? Ga abin da doka ta ce

Tinubu ya yi magana kan rasuwar marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu
Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar marigayi Rotimi Akeredolu. Hoto: Bola Tinubu, Rotimi Akeredolu.
Asali: Twitter

Mene Tinubu ke cewa kan rasuwar Akeredolu?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin a bangaren yada labarai ta zamani, Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba 27 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce Akeredolu abokinsa ne marar tsoro wanda ya ba da gudunmawa matuka ga ci gaban jihar Ondo.

Shugaban ya bayyana irin gudunmawar da Rotimi ya bayar lokacin da ya ke shugaban kungiyar NBA wurin tabbatar da bin doka.

Ya kuma yaba da gudunmawar da ya bayar lokacin da ya ke kwamishinan Shari'a a jihar da kuma lokacin mulkinsa a matsayin gwamnan jihar.

Tinubu ya tura sako ga mataimakinsa mai jiran gado

A cikin sanarwar Tinubu ya ce:

"Na kira matarsa, Betty da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa na jajanta musu da cewa su dauki hakurin wannan rashi.

Kara karanta wannan

Rotimi Akeredolu: Jerin gwamnonin Najeriya da suka mutu a ofis da musabbabin mutuwarsu

"Gwamna Akeredolu ba aboki ne a wuri na ba, Rotimi dan uwa ne kuma masoyi na hakika, tabbas jami'yyar APC ta yi rashin jajirtacce.
"Ina fatan mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa zai ci gaba da aikin alkairi kamar yadda marigayin ya fara a farko."

Gwamna Akeredolu ya rasu

A wani labarin, a safiyar yau Laraba ce aka tashi da mummunan labarin rasuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Rotimi ya rasu ne a daren jiya Talata 26 ga watan Disamba bayan ya sha fama da jinya mai tsawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel