Rotimi Akeredolu: Jerin Gwamnonin Najeriya da Suka Mutu a Ofis da Musababbin Mutuwarsu

Rotimi Akeredolu: Jerin Gwamnonin Najeriya da Suka Mutu a Ofis da Musababbin Mutuwarsu

  • A yayin da ake ci gaba da jimamin mutuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, Legit ta tattaro bayani kan gwamnonin da suka mutu a ofis
  • Rahoton ya yi duba ne kan sabubban mutuwar gwamnonin da kuma matakin da jihohinsu suka dauka bayan mutuwarsu
  • Dangane da Akeredolu kuwa, Legit Hausa ta zakulo wasu muhimman abubuwa 28 da ya kamata 'yan Najeriya su sani akan marigayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Akure, Ondo state - Marigayi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya shiga cikin jerin gwamnonin Najeriya da suka mutu a kan mulki tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960.

Arakunrin Akeredolu ya zama gwamna na hudu da ya rasu a kan karagar mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar Akeredolu, jigon APC ya bayyana wanda za a rantsar a matsayin sabon gwamnan Ondo

Gwamnoni 4 da suka mutu a ofis
Akeredolu, Yakowa, da sauran gwamnonin da suka mutu a ofis, musabbabin mutuwar. Hoto: @RotimiAkeredolu/@Danee_nk
Asali: Twitter

A cikin wannan labarin, Legit.ng ta tattara jerin sunayen wasu gwamnonin Najeriya da suka mutu a lokacin da suke kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Patrick Ibrahim Yakowa

Aljazeera ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kaduna na lokacin, Patrick Ibrahim Yakowa ya rasu ne tare da wasu mutum biyar a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a Ogbia, jihar Bayelsa a shekarar 2012.

Gwamnan Kaduna kirista na farko, Yakowa ya maye gurbin Namadi Sambo bayan ya zama mataimakin shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Wani mazaunin garin da ya shaida hatsarin ya ce jirgin mai saukar ungulu ya yi ta watangaririya a sararin samaniya kafin ya fado cikin dajin.

Mamman Ali

Mamman Ali, gwamnan jihar Yobe na lokacin ya rasu ne a wani asibitin Florida dake kasar Amurka a shekarar 2019 makonni biyu da zuwa kasar domin jinya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 28 da ya kamata ku sani game da marigayi gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

Ali ya karbi rantsuwar kama aiki ne a watan Mayun 2007 n a karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), in ji jaridar AllAfrica.

Shehu Kangiwa

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Shehu Kangiwa ya rasu ne a ofis a wani hatsarin Polo a watan Janairun 1982. Kangiwa shi ne gwamnan jihar Sokoto a lokacin da ya rasu.

An rantsar da mataimakin Kangiwa, Garba Nadama a matsayin gwamnan Sokoto har zuwa watan Nuwamba 1983 lokacin da Muhammadu Buhari ya karbi mulki ta hanyar juyin mulkin soja.

Abubuwa 28 game da Oluwarotimi Odunayo Akeredolu

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa mutuwar Akeredolu ta jefa ‘yan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali bayan da ya fara nuna alamun samun sauki daga jinyar da ya dade yana yi.

Yayin da ‘yan uwa da abokan arziki da ‘yan Najeriya ke ci gaba da karrama jarumin, Legit Hausa ta kuma bayyana wasu abubuwa 28 masu ban sha’awa da ya kamata a sani game da Akeredolu.

Kara karanta wannan

Abin da shugaba Tinubu ya fadawa gwamnonin Najeriya a Legas

An fara shirin rantsar da sabon gwamnan Ondo

Jim kadan bayan sanar da mutuwar Akeredolu, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wani jigo a jam'iyyar APC ya sanar da cewa an fara shirin rantsar da sabon gwamnan jihar Ondo.

A cewar jigon jam'iyyar, za a rantsar da mataimakin gwamnan na yanzu, Lucky Aiyedetiwa matsayin sabon gwamna don ci gaba da jan ragamar mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel