Gwamnan Jihar Arewa Ya Haramta Sha da Sayar da Barasa a Wasu Kananan Hukumomi 9 a Jiharsa
- Gwamnatin jihar Niger ta sanar da haramcin sha da sayar da barasa a wasu kananan hukumomi tara na jihar, ciki har da Suleja
- Hukumar ba da lasisi da sa ido kan tu'ammali da barasa a jihar, ta ce dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, 2024
- Sakataren hukumar, Ibrahim Muhammadu Bonu ya ce za a tashi wasu gidajen giya daga Minna a mayar da su bayan gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Niger - Hukumar ba da lasisi da sa ido kan sarrafa barasa a jihar Niger ta sanar da saka dokar haramcin sha da sayar da barasa a Suleja da wasu kananan hukumomi takwas a jihar.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren hukumar Ibrahim Muhammad Bonu a ranar Litinin, ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, 2024.
Wanda ya sha ko ya sayar da barasa zai fuskanci fushin hukuma
Sanarwar ta bayyana cewa za a tashi wasu gidan giya a Minna, babban birnin jihar don komawa bayan gari, kilomita takwas nesa da ofishin aika wasika na jihar, rahoton Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya ke kira ga duk masu safarar giya su bi dokar da hukumar ta gindaya, Mr Bonu ya ce an fara haramta sha da sayar giya a kananan hukumo tara, kuma Suleja na sahun farko.
Da wannan ya gargadi ma'aikatan hukumar da su gujewa duk wani aikin zamba ko karbar rashawa daga gidajen giya a garuruwan da aka haramta, ko su fuskanci fushin hukumar.
Ya ce:
"Muna kira ga duk masu sayar da barasa su kasance masu bin doka da oda yayin hukumar ta haramta sha ko sayar da barasa a kananan hukumomi tara na jihar, ciki har da Suleja."
Sakataren hukumar ya jaddada cewa hukumar za ta dauki mataki kan duk wanda ya karya wannan dokar.
Yadda bankuna suka wawure N156bn daga asusun 'yan Najeriya
A wani labarin, bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade a Najeriya sun saka naira biliyan 156.94 matsayin kudin harajin VAT a asusun gwamnatin tarayya.
Wani bincike da Legit ta yi ya nuna cewa a watan Janairu zuwa Maris 2023, an wawure naira biliyan 35.40 daga asusun jama'a an saka a asusun gwamnati matsayin haraji.
Asali: Legit.ng