Babban Basarake Ya Kubuta Daga Hannun Yan Bindiga Bayan An Biya N6m da Wasu Abubuwan Ban Mamaki
- Basaraken gargajiya na ƙauyen Nkalagu Obukpa ya shaƙi iskar ƴanci bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da shi
- Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da basaraken ne lokacin da yake shirin naɗin sarautar da aka yi masa
- Majiyoyi sun bayyana cewa sai da aka biya N6m, buhun shinkafa, kwalin giya da sauran kayan abinci kafin a sako shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Basaraken gargajiya na ƙauyen Nkalagu Obukpa da ke ƙaramar hukumar Nsukka ta jihar Enugu, Igwe James Agbogo, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 21 ga watan Disamba, ya samu ƴanci.
Basaraken, wanda aka yi garkuwa da shi a fadarsa, ƴan bindigan sun sako shi ne a ranar Kirsimeti bayan ya shafe kwanaki huɗu a tsare, cewar rahoton The Nation.
Rahotanni daga ƙauyen sun ce an sako sarkin ne bayan da iyalansa suka aika da buhun shinkafa ɗaya, ƙatuwar kaza guda ɗaya, kwalin giya da sauran kayan abinci da jimillar N6m ga waɗanda suka sace shi a matsayin kuɗin fansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Leadership ta ce Agbogo dai na shirin naɗin sarautar da za a yi masa ne a a ranar 28 ga watan Disamba, lokacin da masu garkuwa da mutanen suka sace shi.
Ta wacce hanya basaraken ya kuɓuta?
"Igwe ya samu ƴanci a jiya (ranar Kirsimeti) amma an kai shi asibiti domin yi masa magani." A cewar wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa:
"Satar sa ta baƙin ciki ta faru ne a Nkalagu Obukpa a daren ranar Alhamis ɗin da ta gabata da misalin ƙarfe 8:00 na dare. Kun san yana shirin naɗin sarautarsa a ranar 28 ga Disamba, 2023 bayan an zaɓe shi a matsayin Igwe."
"Amma wani abin ban dariya game da sace shi shi ne, mutanen sun buƙaci a ba su kudi Naira miliyan 6 kuma sun dage cewa sai an haɗa da buhun shinkafa kwalin giya da sauran kayan abinci ko kuma su kashe shi."
"To, kowa ya yi ƙoƙarinsa wajen samar da komai domin Igwe ya samu ƴancinsa."
Ƴan Bindiga Sun Halaka Mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan hari a jihar Sokoto tare da halaka mutum 12.
Ƴan bindigan a harin da suka kai a ƙaramar hukumar Rabah, sun ƙona wata mata da surukarta da ƴaƴanta biyu da ransu a cikin ɗaki.
Asali: Legit.ng