“Ku Rage Kashe Kudi”: An Hasasho Yadda Talaka Zai Sha Wahala a 2024, Tattalin Arziki Zai Lalace

“Ku Rage Kashe Kudi”: An Hasasho Yadda Talaka Zai Sha Wahala a 2024, Tattalin Arziki Zai Lalace

  • An shawarci 'yan Najeriya da su fara tanadin abinci da rage kashe kudi yayin da ake shirin shiga shekarar 2024 wacce ka iya zuwa da matsin rayuwa
  • Wani masanin tattalin arziki Farfesa Uba ya ce alkaluma sun nuna cewa 'yan Najeriya za su kara fuskantar tabarbarewar tattalin arziki
  • A cewar Uba, ya zama wajibi mutane su rage kashe kudi, la'akari da cewa akalla 'yan Najeriya miliyan 133 ke rayuwa cikin talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Enugu - Wani shahararren mai fashin baki kan tattalin arziki Farfesa Chiwuike Uba ya ce 'yan Najeriya za su shiga mawuyacin hali a shekarar 2024 saboda tabarbarewar tattalin arziki.

Akan wannan, ya ba 'yan Najeriya shawara da su rage yawan kashe kudi tare da daukar matakan alkinta abin da suka tara.

Kara karanta wannan

Za mu shawo kan dukkan matsaloli tare da karfafa Najeriya - Ganduje

Za a yi fatara a Najeriya a 2024
Farfesa Chiwuike Uba ya ce 'yan Najeriya za su shiga mawuyacin hali a shekarar 2024. Hoto: Aljazeera, Acufng
Asali: Facebook

Mutane miliyan 133 ke rayuwa cikin talauci a Najeriya

Da ya ke zantawa da kamfanin dillacin labarai (NAN) a Enugu a ranar Talata, Uba, ya yi nuni da cewa tallain arziki zai kara lalacewa, rayuwa za ta yi tsada a shekara mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tariyo rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) da ya nuna cewa kaso 62.9% na 'yan Najeriya (kusan mutum miliyan 133) na rayuwa cikin talauci, don haka akwai bukatar daukar matakai kafin shekarar 2024 ta fara.

Kari kan hakan, akwai hauhawar farashin kayan masarufi da kaso 28.20% a watan Nuwamba 2023 wanda ke nuni da cewa 2024 ba za ta zo wa 'yan kasar da dadi ba, rahoton Leadership.

Me ke jawo 'yan Najeriya ke yawan kashe kudi?

Uba ya nuna damuwarsa kan yadda wasu 'yan Najeriya musamman talakawa ke da dabi'ar kashe kudi don kece raini ba tare da hasashen abin da ka iya zuwa ya dawo ba.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Ya kuma kara nuni da yadda wasu ma'aikatan gwamnati ke kashe kudi ba gaira babu dalili duk da sun san suna samun kudin ne karshen wata kawai, wanda hakan barazana ne.

Yayin da ya ke bayani kan dalilan da ke sa mutane kashe kudi barkatai, ya ce akwai dabi'ar son burge mutane da kuma dora wa kai abin da mutum ba zai iya ba.

Jerin jihohin Najeriya da suka fi tsadar abinci - Rahoto

Legit Hausa ta yi nazari kan jihohin da aka fi samun saukin kayan abinci, da kuma wadanda suka fi tsadar kayan abincin a fadin Najeriya.

Jihar da aka fi tsadar kayan abinci ita ce jihar Kogi, da kaso 42 cikin 100, sai kuma jihar da kayan abinci ke da sauki ita ce jihar Kebbi, da kaso 25 cikin 100

Yan Najeriya na iya amfani da wannan kididdigar don zama haske gare su idan suka tashi sayen kayan abinci

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.