Kirsimeti: Yan Shi’a Sun Halarci Bikin a Coci, Sun Fadi Kwararan Dalilai Masu Kama Hankali

Kirsimeti: Yan Shi’a Sun Halarci Bikin a Coci, Sun Fadi Kwararan Dalilai Masu Kama Hankali

  • Kungiyar Shi’a ta kai ziyara coci a jihar Kaduna don taya al’ummar Kirista bikin Kirsimeti yayin da ake ci gaba da bukukuwan
  • ‘Yan kungiyar sun halarci bikin Kirsimetin ne a cocin St. Joseph a Samaru da ke birnin Zaria a jihar
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan kungiyar Islamic Movement da aka fi sani da Shi'a kan wannan lamari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – ‘Yan kungiyar Shi’a a Najeriya sun taya al’ummar Kiristoci murnar Kirsimeti a jihar Kaduna.

Yan kungiyar sun halarci bikin Kirsimetin ne a cocin St. Joseph a Samaru da ke birnin Zaria a jihar.

Yan Shi'a sun taya al'ummar Kiristoci bikin Kirsimeti coci
Yan Shi’a Sun Halarci Bikin Kirsimeti a Cocin Kaduna. Hoto: Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Asali: Facebook

Mene dalilin ziyarar Shi'a zuwa coci?

Kara karanta wannan

Inna lillahi: An sake kai hari wata jihar Arewa, an kashe mutum biyu tare da yin mummunar barna

Kungiyar ta bayyana cewa ta yi hakan ne don karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin addinan guda biyu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran kungiyar, Farfesa Isah Hassan Mshelgaru ya ce kungiyarsu ta na shiga bikin ne don nuna abota da kuma zaman lafiya.

Mshelgaru ya ce matakin da suka dauka na zuwa cocin sun yi ne inganta alaka mai kyau a tsakanin addinan guda biyu da suka kunshi kasha 90 na mutanen kasar.

Mene Faston cocin ya ce kan ziyarar Shi'a?

Ya ce:

“Duk lokacin da aka ce dayan addinin ya hadu da sauran guda biyun, ta tabbata duka kasar ta zama daya kenan.
“Ziyarar an yi ta ne don rage tsoro a tsakanin addinan, Kiristocin sun tarbe mu inda muka tattauna matsaloli da dama kuma muka dinke Baraka.”

Tun farko a jawabinsa, Rabaran Isak Augustine ya yabawa kungiyar kan wannan ziyara inda ya bukaci ci gaba da irin wannan alaka a gaba.

Kara karanta wannan

"Ku rage kashe kudi": An hasasho yadda talaka zai sha wahala a 2024, tattalin arziki zai lalace

Ya yi addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya da kuma kare kasar Najeriya daga duk wasu matsalolin kasar, cewar Daily Trust.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai bin tafarkin Shi'a, Ibrahim Abubakar a Gombe kan ziyarar inda ya ce babu wani aibi a ziyarar da suka kai.

Ibrahim ya ce ai ba wani abu ba ne don Musulmai sun kai ziyarar murnar bikin ranar haihuwar Annabin Allah.

Ya ce:

"Ni dai a fahimta ta babu wani laifi don Musulmi sun ziyarci Kirista saboda wasu dalilai kamar haka.
"Na farko, su yan uwan mu ne dukkan mu Ubangiji ne ya halicce mu, a matsayin mu na Musulmi zama ya hada mu dasu nauyi ne a kan mu mu yi zaman lafiya."
"Allah ya halatta mana cin abincin su, da ma auren su a cikin Suratul Ma'idah aya ta 5, haka nan aya ta 82 Allah ya sake tabbatar mana da cewa sun fi kusa ga kaunar Musulmai akan Yahudawa.

Kara karanta wannan

Musulmai sun taya Kiristoci bikin Kirsimeti a jihar Bauchi

"Tarihi ya tabbatar da cewa Manzon Allah (SAW) ya yi zaman lafiya da Kiristoci ya nuna musu tausayawa, bai kyamace su ba."

Yan Shi’a sun nemi adalci kan harin bam

A wani labarin, Kungiyar Shi’a a Najeriya ta bukaci a yi adalci kan wadanda suka kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna.

Wannan na zuwa ne bayan sojoji sun jefo bam kan wasu a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.